Connect with us

WASANNI

Bale Zai Koma Kasar China Da Buga Kwallo

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Sin wato China, sun bayyana cewa wata kungiya wadda har yanzu ba a bayyana sunanta ba ta yi alkawarin za ta nin kawa dan wasan Real Madrid, Gareth Bale, albashinsa idan har ya amince zai koma kungiyar da buga wasa a kakar wasa mai zuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta bayyana cewa bazata cigaba da zama da dan wasan ba kuma shi kansa kociyan kungiyar, Zinadine Zidane ya tabbatar wa da dan wasan cewa baya cikin tsarinsa a kakar wasa mai zuwa.

Sai dai dan wasa Bale ya ce yana kan bakarsa cewa shima bazai bar kungiyar ba har sai an samu kungiyar da zata dinga biyansa irin albashin da yake dauka a Real Madrid kuma yana da ragowar kwantiragin shekara uku a kungiyar.

Sai dai wata kungiya daga kasar China tayi alkawarin zata cika masa burin nasa saboda zata bashi abinda yake bukata kuma tayi alkawain zata ninka masa albashin abinda yasa ake ganin watakila Bale zaiyi tunanin tafiya.

Sai dai kungiyar kuma ta bayyanawa Real Madrid cewa bazata biya kudin sayan dan wasan da yawa ba saboda Madrid din ce take neman kai da dan wasan nata wanda ya shafe shekaru shida yana bugawa kungiyar wasa.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana daga kasar Sipaniya, a jiya wasu magoya bayan kungiyar Real Madrid sun taru akan hanya suka zazzagi dan wasan dan asalin kasar Wales akan hanyarsa ta tafiya filin daukar horo saboda yaki barin kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: