Connect with us

LABARAI

Tarin Fuka: Tallafin Gwamnatin Tarayya Da Na Masu Zaman Kansu Bai Isa Ba – Kwararru

Published

on

Taimakon da gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin bayar da tallafi na Duniya suke bayarwa a kan yaki da cutar TB (tarin fuka), a kasar nan sam baya isa, kwararru ne suka shaida hakan. Sun bayyana hakan ne a Abuja, sa’ilin da suke yi wa manema labarai bayani a wajen taron masana a kan tarin na Fuka da kuma taron cin abincin dare na kwararrun a kan cutar TB da kungiyar, Stop TB Partnership Nigeria, ta shirya.

Shugaban kungiyar ta, Stop TB Partnership Nigeria, Farfesa Lobett Lawson, ya ce, kasar nan tana bukatar taimakon sama da kashi 76 a kan cutar TB in an kwatanta da abin da take bayarwa a halin yanzun da kuma matsayin da cutar ta TB ta kai a cikin kasar nan daga yanzun zuwa shekarar 2030.

Sauran sassan da ake amun kudaden suna da bukatar ganin Nijeriya ta kai ga samar da hakan,” in ji shi. Ya ce abu dan kadan ne za a yi a saka kamfanonin mai da iskar gas kamar yanda aka yi a sauran kasashen domin cike gibin tallafin da ake nema din.

Ya yi nuni da cewa, a sakamakon hakan ne, kungiyar na su ta, Stop TB Partnership Nigeria, tare da hadin gwiwar wasu masu ruwa da tsaki suka shirya liyafar cin abincin dare a Legas, a ranar 14 ga watan Yuli, domin su shaidawa manyan shugabannin kamfanonin halin da ake ciki dangane da cutar ta TB.

Ya ce, taron cin abincin daren, Gwamnan Jihar Legas ne da sauran manyan masu ruwa da tsaki za su karbi bakuncinsa. Jihar Legas ce ke da babban nauyi a kan cutar ta TB, a Nijeriya.

Makasudin kungiyar shi ne kara wayar da kai a kan cutar ta TB da janyo hankali a siyasance. A kuma kara tallafin da ake bayarwa a kan magance cutar ta hanyar yin amfani da kamfanoni domin su taimaka wa masu cutar.

Farfesa Lawson, ya kuma shelanta taron da za a yi a kan cutar ta TB mai taken, ‘’Building Stronger Partnerships to End TB in Nigeria’’ wanda za a yi a babban dakin taro na duniya na kasa daga ranar 17 zuwa 18 ga watan Yuli, yana mai cewa, taro irinsa an yi shi ne na karshe a ranakun 17 da 18 na watan Mayu, 2016.

Babban shugaban kula da cutar ta TB a ma’aikatar lafiya ta kasa, Dakta Adebola Lawanson, wanda Dakta Ahmad Muhammad Ozi, ya wakilce shi ya ce, Nijeriya da kasar Indiya ne suke da kashi 48 na masu fama da cutar ta TB a duk fadin Duniyar nan, su ne kuma ke da kashi 43 na masu mutuwa a sanadiyyar cutar a Duniya.

Ta ce, a shekarar 2017, Nijeriya ta sami rahoton masu fama da cutar ta TB har guda 104,904, ta kara da cewa, yara ‘yan tsakanin shekaru, (0-14) ne suka fi kamuwa da cutar da kashi 7 a shekarar 2017.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!