Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Wajabta Wallafa Fasfon Nijeriya A Kamfanin Buga Kudi Na Kasa

Published

on

Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi umurni da a rika wallafa dukkanin katunan sabon Fasfo na kasar nan da mahimman takardu makamantan hakan a kamfanin da ake buga takardun kudi na kasar nan, Nigerian Security Printing & Minting Company (NSPMC).

Kamfanin wanda aka fi da kira da, The Mint, an kafa shi ne a shekarar 1963, da manufar ya rika buga takardun kudin da ake kashewa a kasar nan ga babban bankin Nijeriya, gami kuma da wasu mahimman takardun gwamnati da suka shafi na tsaro ga ma’aikatun gwamnati da sauran hukumomin gwamnati, har ma da bankuna da wasu mahimman kamfanonin gwamnati.

Da wannan sabuwar dokar wacce ta fito daga shugaban kasa, dukkanin wasu takardun yarjeniyoyi da na ayyukan kwangila da suka shafi wallafa na hukumomi da na kamfanoni ba za a canza su ba.

Kamfanin shi ne babban wajen da ake buga takardun kudi da mahimman takardu na gwamnati mafi girma a duk fadin yammacin Afrika. Sai dai, ayyukan na shi suna ta kara ja baya musamman a fannin buga kudi da mahimman takardu baya ga shekarar 2014.

Kamfanin wanda yake a karkashin shugabancin gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, an sanya masa sabuwar manufa ne, da kuma sabon shugaban da zai kula da shi, Abbas Masanawa, wanda ya lissafta wasu daga cikin nasarori da suka hada da rashin biyan ko sisi wajen shigo da sabbbin takardun kudin da aka buga daga waje, tun daga shekarar 2014 zuwa yanzun,kamar yanda ake yin hakan a kafin wannan lokacin.

Masanawa ya ci gaba da lisafta nasarorin kamar haka; “Kamfanin ya zama wata kafa ta samun riba. Sabanin yanda yake a mai zaman banza a can baya, wanda yake ta tafka asara, kamfanin ya tashi daga mai yin asarar naira milyan 14.6 a shekarar 2014 zuwa mai cin ribar naira bilyan 14.3 a shekarar 2018. Hakanan jarin kamfanin ya haura daga naira bilyan 17.8 a shekarar 2014 zuwa naira bilyan 61.4 a shekarar 2018.

Sauran nasarorin da kamfanin na buga kudin ya samu sun hada da, bunkasa yawan abin da yake iya bugawa, samar da hanyoyi daban-daban na shigan kudi, rage tsadar aiki, tsara buga mahimman takardun kamfanonin gwamnati, inganta yalwatawa ma’aikata da gudanar da ayyuka a kan ka’idan aiki da makamantansu.

Jami’in ya yi alkawarin cewa, kamfanin wallafa kudaden zai dawo da martabar da shugaban kasa ya dora masa,” a daidai lokacin da muke shiga zuwa mataki na gaba, muke kuma kokarin kara samar da tsaro da kiyaye mutuncin kasarmu, za mu taskace ajiyar kudadenmu na waje, mu inganta hanyoyin samun kudaden shiga, samar da ayyuka, da samar da hanyoyin koyon fasahohin zamani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: