Connect with us

LABARAI

Jama’atud-Da’awah Ta Yi Taron Bita Ga Maniyyata Hajjin Bana A Abuja

Published

on

A wannan makon ne, qungiyar jama’atu-da’awah ta gudanar da taron bita ga maniyyata aikin hajji.

Wannan taro ya guda ne a makarantar Fou’ad Lababidi Islamic Academy da ke zone 3, Abuja. Taron ya samu hallartar maniyyata aikin hajji maza da kuma mata. Qungiyar ta bakin shugabar reshen mata, Hajiya Rakiya Bamalli, ta bayyana maqasudin gudanar da wannan taron bitar ga maniyyata aikin hajji, inda ta bayyana cewa, sau da yawa mahajjata kan gudanar da aikin hajji ba tare da sanin yadda ake yin ibadar ba.

“Wannan ne ya sa qungiyar ta dauki matakin ilmantar da maniyyata, domin su gudanar da aikin hajji karbabbiya. Wannan taro na Jama’atud-d’awa shi ne kusan na 16. Duk sanda aka riski irin wannan lokaci ya zo dai-dai da na aikin hajji, qungiyar kan tara maniyyata domin ta ilmantar da su ta yadda za su yi aikin hajji karbabbiya.  Lallai shi aikin hajji daya ne daga cikin rukunnen musulunci guda biyar wanda Allah ya daura wa musulmai ga duk wanda Allah ya  ba shi ikon, kuma duk cikin musulunci babu wata ibada da take da dokoki da ake so mutum ya sa kula kamar aikin hajji, shi ya sa ake so mutum ya sami cikakken ilimi akan ta. Shi ya sa qungiyar ta ga ya dace ta ilmantar da maniyyata aikin hajji, don su yi aikin hajji wanda Allah zai karba”. 

Babban malamin da ya gabatar da bitar ga maniyyata, Ustaz Malam  Muhammad Kabir Usman, ya yi bayanin aikin hajji tun daga niyya har zuwa qarshe, sannan kuma ya zo ya yi shi a aikace dalla-dalla ta yadda  maniyyata za su fahimta. Ya gudanar da bayaninsa ne a kan aikin hajji daban, sannan ummara ma daban.

Ya fara bayani kamar haka; “za a fara daukar niyya sai kuma a fadi niyyan a baki, sai a yi wanka iri na ibada, sannan sai dawafi. Ana fara dawafi ne a Hajrul Aswad sai a zagaya sau bakwai, bayan an gama sai a yi sallah raka’a biya a wajen maqama Ibrahim, sannan sai a tafi sa’ayi a yi dawafi, shi kenan an gama ummara, sai kuma aikin hajji.

“Ana fara daukan niyya ne na aikin hajji tun daga ranar 8 ga watan Zulhijja, za a fara zuwa Mina. Ranar 9 ga wata kuma sai a tafi filin Arfa, ba za a bar filin arfa ba har sai rana ta fadi, sannan a dawo Musdalifa a ranar 10 ga wata, inda za a yi jifa. Ana fara jifa ranar 10-11- 12 wadan suma har 13 kafin su koma Mina. Sai kuma dawafi da sa’ayi kamar yadda aka yi na ummara haka za a yi shi ma na aikin hajji babu wani bam-bamci,” ya bayyana.

Har ila yau, Malam Kabir ya shawarci maniyyata da su sayi duk wani abun da suke amfani da shi na yau da kullum a Nijeriya kamar su; sabulun wanka, buroshi, man wanke baki, sosan wanka, salifas da dai sauran su. Domin sun fi tsada a qasa mai tsarki, don kada kudinsu ya yi qaranci. Haka ma idan mutum yana fama da wata cuta kuma yana shan magani, to ya sayi maganinsa tun a Nijeriya, domin zai iya yiwuwa babu wannan maganin a can qasa mai tsarki ko kuma idan ma akwai sai ka ji ya yi tsada fiye da na Nijeriya.

Ya qara da cewa babbar abin da maniyyaci zai yi guzuri da shi, shi ne tsoron Allah. Kamar yadda Allah mai girma ya fadi a cikin Alqur’ani, sannan su kyautata niyyansu tsakanin su da Allah.

Daga qarshe maniyyatan sun gabatar wa malamin tambayoyinsu, inda ya yi musu bayani dalla-dalla. 

Maniyyatan sun bayyana godiyarsu ga qungiyar Jama’atud-Da’awa wajen qoqarin da suka yi na ilmantar da su musamman ma Malam Kabir Usman da ya dauki dogon lokaci yana masu bayani, sannan kuma ya zo ya yi shi aikace domin maniyyatan su fahimta.

Sun kuma sha alwashin yin aiki da abin da malamin ya karantar da su idan suka zo gudanar da aikin hajjin. 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: