Connect with us

LABARAI

Matasa Sun Sace Yaro, Sun Kashe Shi A Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta cafke wasu matasa uku da take zargi da sace wani yaro dan shekara biyar a Unguwar Karkasara. An sace yaron ne da hadin bakin wanda ke raka shi makaranta, inda suka nemi a basu naira miliyan 50, a cewar Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Iliyasu.

Bayanai sun ce wadanda suka sace shi sun ba shi kwayoyi sannan suka daure masa baki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa, sannan suka binne shi a wani kango.

BBC Hausa ta labarto cewa; “Da jin labari sai muka bazama nemansu, kuma muka kama daya daga cikinsu wanda ta dalilinsa ne muka kai ga cafke ragowar,” a cewarsa.

Kwamishina Ahmed Ilyasu ya ce mutuwar yaran ce ta sa suka rage kudin da suka nema zuwa 100,000. Ya kara da cewa “dubunsu ta cika ne bayan da suka fito karbar kudin da suka nema, inda ma’aikatanmu suka yi musu kwantan-bauna, sannan muka kama su.”

‘Yan sanda sun kuma tono gawar yaran, wadda suka ce babu abin da ya same ta. Abin takaici da rashin imani shi ne barayin, wadanda shekarunsu suka kama daga 19 zuwa kasa, na “da alaka da iyayen yaran ne,” in ji shugaban ‘yan sandan na Kano. Kwamishina Ilyasu ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Batun satar mutane domin karbar kudin fansa na ci gaba da bazuwa a sassan Nijeriya daban-daban. Wannan ne ya sa kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga jama’a da su rinka lura da irin mutanen da suke hulda da su, domin bayar da bayani ga hukumomi da zarar sun ga wani abu da ba su gamsu da shi ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: