Connect with us

LABARAI

Ya Kamata ‘Yan Majalisa Su Ba Shugaban Kasa Hadin Kai – Alhaji Mani

Published

on

A hirar da ya yi da Leadership Ayau, Alhaji Usman Mani lokacin da aka tambaye shi dangane da karo na biyu, ko kuma wa’adi, sai ya bayar da amsar cewar yana sa ran kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutumin kirke ne, mai gaskiya da rikon amana. Ko shakka babu a cikin wa’adin shi na farko ya taka rawar gani, ta bangarori daban- daban, koda-yake dai shi mutum tara yake bai cika goma ba, yana kuma kira gare shi, a wuraren da ya san ya yi kurakurai, da cewar ya yi kokari ya gyara su.

Da kuma aka zo kan maganar irin mutanen da shi Shugaban kasa ya kamata ya ba mukaman  ministoci sai ya bayyana cewar, ya dace ka da duk ya damu da maganar da jama’a za su yi, amma kuma duk wani abin da ya san zai kasance ma kasa alkhairi, ya yi kokarin aiwatar da su. Ina nufin ya zabo mutane masu gaskiya, hazikai, da kuma rikon amana, ka da ya bayar da sunayen mutanen da su ba abin da suka sani daga su sai ‘ya’yansu. Ko kuma su rika tafiya zuwa kasashen  waje yin abubuwan da ba su ba ne damuwar  ‘yan Nijeriya, da kuma sayen  kaddarori. Ya kuma ci gaba da bayanin cewar, ya dace a bi cancanta wajen zaben wadanda za a ba mukaman Ministoci, ya ce  babban abin da yake so shine, a zabo ‘yan siyasa, saboda su suka san yadda ake tafiyar da al’amuran siyasa sosai da kuma yadda damuwarta take, musamman wajen tafiyar da abokansu na siyasa. Su kuma ‘yan boko akwai mukaman da suka kamata a ba su, ya kuma yi kira ga wadanda za a ba mukaman  na Ministoci, su ji tsoron Allah wajen yadda za su tafiyar da ayyukan su.

Dangane kuma da su ‘yan majalisa irin gudunmawar da ta kamata su ba shi Shugaban kasa wajen tafiyuar da ayyukan shi, sai ya bayar da amsar cewar, babban farin ciki shi ne yanzu an zabi ‘yan jam’iyyar APC ne, ba irin wancan lokacin ba wanda aka yi gamin gambiza, shi kuma Shugaban kasa bai samu hadin kan da ya dace su ba shi ba. Yana kuma iya tunawa shi Shugaban majalisar dattawa ba wani tsohon gwamna bane, bare a ce zai ji shakkar wani ko kuma wasu. Hakanan ma shi  Shugaban majalisar  wakilai ta kasa shi ma dan jam’iyyar APC ne hakika, duk babu wasu shakku dangane da su. Ya yi kira gare su da su ba shi hadin kai wajen yadda za a tafiyar da kasar Nijeriya, su kuma tafiyar da aikin su cikin gaskiya da rikon amana, su gina kasa kamar yadda ya kamata. A tsare kasa da kuma taimakonta su kuma talakawa ka da a manta da abubuwan da suka kamata a yi masu. Wato musamman ayyukan da za su kawo ci gaban su, kamar samar da hanyoyi, ruwan sha, wutar lantarki, makarantu, harkar tsaro, da kuma duk abubuwan da su ‘yan majalisar suka san idan su aikata su, za su kawo ci gaban al’umma.

Bugu da kari kuma ya yi kira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar kudaden da ya tara tun lokacin wa’adin shi na farko, don haka wannan lokacin a fto da kudaden domin a yi ma Talakawa ayyukan da za su kawo masu ci gaba da kuma kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: