Connect with us

LABARAI

Yawancin Matan Nijeriya Ba Su Samun Damar Yin Tsarin Iyali – UNEPA

Published

on

Gidauniyar kulawa da yawan jama’a da kuma ci gaba a karkashin majalisar dinkin duniya, UNEPA ta yi kira ga kasar Nijeriya cewar ta kara zage damtse domin tabbatar da, an dauki wasu sababbin hanyoyi wadanda za su yi maganin mutuwar mata masu juna biyu. Dukkan matsalolin da ake fuskanta dangane da hakan kamata ya yi, ace an samu kawo karshensu, sai kuma shiga tsarin iyali da kuma tabbatar da an ganin ana daina yin dabi’ar nan ta yadda ake zaluntar wani jinsi hakanan.

 Jami’in asusun da ke karkashin majalisar dinkin duniya wanda ke kulawa da al’amarin na Nijeriya Mista Edward Kalion, shine wanda ya yi wannan kiran, wajen bikin na gidauniyar wanda ta cika shekaru hamsin, da kuma taron da aka yi a kasar Masar shekaru 25 da suka wuce na ICPD. Watau taron yadda za a tunkari yawan jama’a na duniya da kuma ci gaban su a shekarar 1994.

Ya ci gaba da bayanin cewar duk kuwa da yake akwai ci gaban da aka samu tun daga shekarar ta 1994, wani abu daya wanda ya rage shine, har zuwa yanzu ba a cimma muradin matakin da aka dauka, a taron na Cairo wanda ake sa ran duk al’ummar duniya za su yi amfana da shi muddin idan an aiwatar da matakin da aka dauka. Kamar dai yadda ya ci gaba da bayani, shi ci gaba kamata ya yi ko wane sako da lungu ya san cewar shi ma ana yi da shi. Ga kuma mata da ‘yan mata har yanzu shi burin nan da ya kamata ace an cimma mawa, ba su san ma halin da ake ciki ba.

Kasashen duniya mata 800 da yawa suna mutuwa  ko wacce rana a sanadiyar matsalolin da suke fuskanta, lokacin da suke da Juna Biyu wato Ciki da kuma haihuwa. Sai kuma wasu 111 wadanda suke mutuwa ko wacce rana lokacin haihuwa. Bayan nan ma da akwai yanzu mata miliyan 214 wadanda su ba su son daukar Ciki, sai dai kuma ba su son yin amfani da maganin hana haihuwa na zamani.

A kasar Nijeriya daya daga cikin mata hudu wadanda suke son amfani da maganin hana daukar ciki, ba su da hanyar da za su yi hakan. Bugu da kari kuma akwai miliyoyin mata wadanda matsalar yake- yake ta shafa, da kuma sauran matsaloli daban- daban ba za su iya haihuwa ba.

Ya yi karin haske wanda yake nuna duk da yake su kasashen duniya suna dai imanin za su iya cimma shi burin, wato na muradan ci gaba ko kuma SDG nan da shekara tya 2030. Da akwai dai ita maganar matakin da aka dauka lokacin taron ICPD a Cairo babban birnin kasar Masar. Sai kuma yadda ake ta yi ma mata fyade fiye da yadda al’amarin yake faruwa a shekarun da suka gabata. Shi dai taron ana sa ran za a yi shi tsakanin ranakun zuwa 15 ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2019 a Nairobi babban birnin kasar Kenya. Wadanda kuma ake sa ran za su halarce shi taron sun hada da gwamnati da kuma wadanda suke zaman kansu, sune kuma sukje da ruwa da tsaki akan shi al’amarin. Sai kuma shugabannin ma’aikatu na jihohi, sai kuma kungiyoyi masu zaman kansu, da kuma shugabannin matasa kamar dai yadda ya bayyana
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: