Connect with us

WASANNI

Barcelona Ta Sayi Sabon Lampard

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sayi dan wasan tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 16 Louie Barry, wanda ake kira Sabon Lampard, kan kwantiragin shekara uku daga kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion mai buga gasar Championship.

Barry ya kasance a West Brom tun yana dan shekara shida amma yaki amincewa ya bugawa babbar kungiyar inda yaso barin kungiyar kuma kungiyoyi da dama da syka hada da Manchester City da Real Madrid sunyi zawarcin matashin dan wasan.

West Brom za su samu fan dubu 235,000 a matsayin lada daga Barcelona, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters kuma  Barcelona ta ce Barry zai buga wa tawagarta ta ‘yan kasa da shekara 19 a kaka mai zuwa.

“Munyi babban rashin na maatshin dan wasa kamar Barry saboda nan gaba zai zama babban dan kwallo a duniya wanda duniya zatayi alfahari dashi kuma munso ace ya amince zai cigaba da bugawa kunhiyarmu wasa” in ji Machael Roop, shugaban kungiyar Westbrom

Ya cigaba da cewa “Amma babu yadda zamuyi saboda abinda yakeso kuma iyayensa sukeso kenan sai dai muna fatan nan gaba kadan zai zama babban dan wasan da zai wakilci kasar Inhila a wasanni daban daban na duniya”

Akwai bukatar West Brom da hukumar kwallon kafa ta FA su amince da cinikin kafin ya tabbata, amma ana ganin hakan ba matsala ba ne sai dai Barcelona ta ce Barry na daga cikin kwararrun matasan ‘yan kwallo a Ingila.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: