Connect with us

LABARAI

Yaki Da Safarar Miyagun Kwayoyi: Buhari Ya Umurci NDLEA Ta Dauki Ma’aikata 5,000

Published

on

Shugaban hukumar NDLEA, Kanal Muhammad Abdallah, ya bayyana cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar hukumar na daukar ma’aikata 5,000 don karfafa ayyukan rundunar a damarar da ta sha na yaki da safafa da kuma shan miyagun kwayoyi a fadin tarayyar kasar nan.

Abdallah ya bayyana haka ne jiya Jumma’a a yayin da aka yi gangamin lalata wasu miyagun kwayoyi da reshen hukumar ta jihar Traraba tayi a garin Jalingo.

Ya kuma kara da cewa, daukar ma’aikatan zai taimaka kwarai da gaske wajen kokarin da gwamnatin Nijeriya take yi na yaki da shan miyagin kwayoyi da kuma safarar ta, abin da ya addabi al’umma musamman a tsakanin matasan Nijeriya.

Daga nan ya kuma kara da cewa, yadda matasa ke kwankwadar miyagun kwayoyi a jihar Taraba na da tayar da hankali, ‘ya kamata iyaye su kawo nasu daukin don ganin an kawo karshen wannnan tashin hankalin.

Daga nan kuma ya kara da cewa, da daga cikin hanyoyin kare matasa daga fadawa shaye shaye shi ne samar musu da ayyukan yi wanda zai dauke musu hankali da kuma sa musu ido a makarantu da wuraren da suke harkokinsu.

Shugaban hukumar ya kuma yaba wa gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a bisa tallafi da taimakon da yake ba hukumar, haka kuma ya jinjina wa matar gwamnan ,Misis Anna Darius, a bisa kokarin da take yin a yaki da shan miyagu kwayoyi a jihar.

Tunda farko, Shugaban hukumar na jihar Taraba, Mista Peter Odaudu, ya ce, hukumar ta lalata fiye da tan 7 (6,963.80 kilogrammes) na tabar wiwi da aka kwace daga hannin matasa a sassan jihar tsakanin watan Janairu na shekerar 2003 zuwa watan Disamba na shekarar 2018.

Ya kuma bayyana cewa, kwayoyin da aka lalata sun hada da Cannabis Satiba da Diazepam da Rophynol, da kuma Tramadol, an kuma samu oda daga kotu na kona kayan mayen gaba daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!