Connect with us

KIMIYYA

Hanyoyi Ashirin Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram

Published

on

Instagram kamar sauran shafukan sadarwa na Intanet ana amfani da shi wajen tallata haja, tunda dai Malam dan Hausa ya ce mai talla shi ke da riba. Idan ka yi ‘searching’ @jiffpom a Instagram wadda take bayyana kanta a matsayin kare, amma yanzu haka tana da mabiya Miliyan Takwas da dubu dari biyar (8.5M) a Instagram kuma tana cikin wadanda ke kan gaba wajen samun kudi a Instagram. Bari na kyale labarinta haka nan, a yau ina tafe da hanyoyi guda ashirin cif! Wanda za su taimaka maka wajen cicciba kasuwancinka a Instagram, sai a biyo ni sau da kafa.

1. Ka yi bayanin kasuwancinka a ‘Bio’ din ‘account’ dinka, ka sanya takaitaccen bayanin abubuwan da kake siyarwa.

2. Ka dinga neman mabiyanka su yi ‘tagging’ din abin da ka saka, zaka ga idan masu tallan kaya a Instagram suka yi ‘posting’ suna rubuta “tag friend”.

3. Ka dinga neman irin masu sana’arka a shafin ka ga yadda suke nasu tsarin, kuma ka dinga ‘tagging’ din su a ‘post’ dinka. Da wannan hanyar Kannywood suka mamaye Instagram a Arewacin Nijeriya.

4. Ba ko yaushe za ka dinga ‘posting’ akan kasuwanci ba, ana son ka dinga yin ‘posting’ na nishadantawa lokaci zuwa lokaci.

5. Ka dinga yin garabasa (Promo) kamar dai a lokutan azumin Ramadan ko Sallah da sauran su.

6. Ka dinga tallata kayanka a ‘comment’ din abokanka. Sannan ka dinga shiga tattaunawar da ta shafi sana’arka.

7. Ka dinga yin “repost” na ‘posting’ din mabiyanka, tamkar kana yaba musu hakan zai sa su dinga daraja kayanka.

8. ‘Account’ dinka ya zama biyu ‘personal’ mai sunanka da kuma na kasuwancinka yadda zaka dinga ‘mentioning’ din kowanne.

9. Ka kaucewa yin duk wani ‘posting’ da bai dace ba, na cin zarafi ko kuma na tada tarzoma.

10. Ka dinga yin ‘posting’ na abubuwan dake da alaka da al’ummar da kake son su siya kayanka.

11. Ka dinga taya ‘followers’ dinka murna a duk raneku kamar sabuwar shekara da makamantansu.

12. Ka dinga amfani da ‘Hash Tag’ na abin da kake siyarwa da abin da ke da alaka da shi da kuma yankin da kake.

13. Ka sanya ‘link’ din tallan kayanka a ‘bio link.’

14. Ka tsara rubutu da hotuna masu kyau wanda za su ja hankali.

15. Ka saka ‘location’ din inda kasuwancinka yake a Instagram din.

16. Ka sanya alamar kira (call) a ‘account’ dinka.

17. Ka dinga saka ‘link’ din kayanka a ‘story’ da ‘Hash Tag’ a ‘story’ din.

18. Ka yi amfani da salon siyar da kaya kyauta, abin da mutum zai biya shi ne kudin kawowa, misali kayan Naira 300 ne kudin, kai ma wanda ya siya kuma Naira 150, to sai ka ce ga kaya yau kyauta kawai kudin kawowa mutum zai biya Naira 500.

19. Ka dinga yin ‘libe bideo’ kana tallata kayanka a ciki.

20. Ka dinga biyan Instagram su tallata maka kayanka.

Wadannan sune hanyoyi ashirin (20) da za su taimaka maka wajen bunkasa harkokin kasuwancinka a shafin sadarwa na zamani na Instagram
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!