Connect with us

JAKAR MAGORI

Wata Mata Ta Shiga Hannu Bisa Zargin Aikata Fashi Da Makami

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Anambra, ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke wata mata mai suna Ifeoma Joy ‘yar shekara 20 da haihuwa, bisa zargin ta da fashi da makami a yankin Eziowelle cikin karamar hukumar Idemili da ke Jihar Anambra. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Haruna Mohammed, shi ya bayyana hakan jiya a garin Awka.

Ya bayyana cewa, an samu nasarar cafke matar ne tare da wani mutum mai suna Ifeanyi Chinweze. Ya kara da cewa, dukkan su wadanda a ke zargi dai ’yar asalin yanki Oranto Ukpo cikin garin Dunukofia, wadanda su ka addabi yankin.

“Bayan samun bayanan sirri, tawagar ‘yan sanda daga yankin Eziowelle tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyar sa-kai masu suna Abatete, su ka samu nasarar cafke mutum biyu wadanda a ke zargin ‘yan fashi da makami ne masu suna, Ifeoma Joy Ugegbe, wacce a ke yi wa lakabi da Sabath da kuma Ifeanyi Chinweze, wanda a ke yi wa lakabi da Cheplat mai shekaru 19 da haihuwa. “An samu nasarar kwato bindiga cike da harsashi daga hannun wadanda a ke zargi.”

Kakakin rundunar ‘yan sandar ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandar ta samu nasarar damke wani mutum mai suna Nwali Chibuzor, bisa sace wa Uche John, motarsa a yankin Nkpor. Ya cigaba da cewa, wanda a ke zargin dan asalin kauyen Eke Nkpor ne da ke cikin karamar hukumar Idemili ta jihar, ‘yan sanda daga yankin Ogidi ne su ka samu nasarar cafke wanda a ke zargin.

Ya ce, “An samu nasarar kwato motar daga hannun wanda a ke zargi a tashar Idemili cikin kauyen Nkpor. Wanda a ke zargin ya canza lambar motar daga Anambra HAL 776 zuwa Inugu NSK 177 KW.”

Mohammed ya ce, za a gurfanar da dukkan wadanda a ke zargi a gaban kotu idan a ka kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!