Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Edo: Wani Mutum Ya Rataye Kansa A Ginin Babbar Kotun Jihar

Published

on

A ranar Talata ce, a ka tsinci gawar wani mutum a kangon ginin babbar kotun Jihar Edo da ke garin Benin babbar birnin jihar. Mamacin mai suna Moses Airhiabonkpa dan shekara 65 da haihuwa, ya na da yara guda biyar, an dai bayyana cewa, ya na da shari’a kan fili a yankin Ugiokhuen cikin karamar hukumar Oredo ta Jihar Edo. Lamarin ya shafi mutane da yawa, inda har da dan’uwar mamacin mai suna Mista Osasu Isoken, ya bayyana cewa, wurin ba mallakar kamfanin A&K Construction Company ba ne.

A cewarsa, “na samu kiran wayar daga wurin ‘yan sanda da safe cewa, an harbe mahaifina ya mutu, lokacin da na isa wurin, sai a ka bayyana min cewa, an samu gawarsa ne a wani kango na babbar kotun, inda jini ya dunga kwarara a wannan kango hawa na daya, ina dubawa sai a ka same shi ya rataye kansa. “Mutuwarsa ta na da alaka da filin da kamfanin ya ke ginawa. Abinda ya faru ya na da nasaba zalinci.”

Isoken ya bukaci hukomomi da su binciki lamarin, domin a yi musu adalci.

Wani dattijo daga yankin mai suna Johnson Obanor, shi ne ya kai lamarin rikicin filin ga kotu, ya bayyana wa manema labarai cewa, mamacin ya bar su lokacin da su ke jiran lauyan da ke kare su, inda daga baya lauyan ya bayyana musu cewa ba za a saurari wannan karar yau ba.

“Mun zo kotu tun da sassafe mu uku a yau, amma lauyenmu da ya zo sai ya ce mu  dan jira na wasu lokuta, domin bai duba lokacin da za a cigaba da sauraron shari’armu. Mamacin da ya rataye kansa shi ne ya bai wa lauyen kudi a yau, “Kafin lauyenmu ya dawo, sai mamacin ya dauki izinin a kan zai je ya yi fitsari. Bayan mun kama jiran shi na wani tsawon lokaci, sai mu ka fara kiran shi a wayar salula, sai dai kuma wayarsa ta na ta kara babu wanda ya dauka, lokacin da mu ka ga wayarsa a inda ya zauna, sai mu ka yi tunanin cewa ya na neman wayarsa ne.   

“Lokacin da mu ka isa hawan ginin na daya, sai mu ka ga mutane su na gudu su na cewa, wani ma’aikaci ya fado daga saman gini. Mu na isa wurin, sai su ka ga ashe dan’uwanmu ne.”

Har zuwa lokacin da a ke hada wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin wakilin kamfanin A&K Construction ba. Amma dai wakilinmu ya labarta mana cewa, masu gadin da ya samu a bakin kofar shiga kamfanin sun tabbatar masa da cewa, akwai shari’a tsakanin mamacin da kuma wannan kamfaninsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: