Connect with us

TATTAUNAWA

Muna Kira Ga Sanata Shekarau Ya Samar Da Zauren Saurarar Jama’a A Mazabarsa – Kwaru

Published

on

An yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yake a zangon mulkinsa na biyu, da ya rika tattaunawa da mutane masu bashi shawara akan abun da ya shafi mulkinsa, saboda kauce wa sake fuskantar matsalolin da aka ci karo da su a  zangon farko na mulkin shugaban, duba da muhimmanci da wannan lokacin yake ga al’umma, Arewa da ma kuma kasa baki daya.

Tsohon dan takarar sanatan Kano ta tsakiya Alhaji Saleh Adamu Kwaru ne yayi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kano, dan takarar sanatan wanda yayiwa jamiyyar (Social Democratic Party) (S.D.P) takarar sanata Kano ta tsakiya ya sha kayi a hannun sanata mai ci Sardaunan kano.

Kwaru ya kara da nuni da cewa shugabancin mai girma Gwamnan Jihar Kano (Khadimul Islam) Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana kokari a kan nade-naden da yake yi yana yi ne don ganin an samarwa da mutane cigaba ba wai kawai don radin kansuba.

Shi ya sanya yake taka tsantsan a kan wadanda zai damkawa amana don samar da shugabanci na gari sannan babban shugabanci daya ragewa mai girma gwamna shine na yayi ko Karin kafa majalisarsa, wanda ana ta lalibe akan su waye za su taimaka masa, inda ya ce muna mai fatan Allah, ya bashi wadanda za su taimakamasa sauke nauyin da al’umma suka dora mai wanda mutane na kwarai masu rikon amana,.

Muna masa kyakkyawan zato a wannan salon na biyu wanda za’a samu bambanci da baya, salon da baya ya gudana.

Daya juya kan nasarar sanatan kano ta tsakiya wanda yake a zauren majalisar dattawa, ya ce, “Muna kara kira ga sanata mal. Ibrahim Shekarau da ya samar da wani zaure na musamman wanda zai dunga ganawa da ainihin mutanensa na kananan hukumomi guda goma sha biyar (15) da yake wakilta, a baya wakilin da ya sauka ba mu taba samun ko da sau daya kira irin wannan zauren ba ya tarasu ya ji su ba, domin samar musu da maslahaba, ya yi kokari ya samar da ofishi jin abubuwa da suke da bukata,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: