Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Cafke Matashin Da Ya Boya A Rufin Banki Da Niyyar Sata

Published

on

Wani matashi ya boye a cikin saman rufin bankin Guaranty Trust Bank (GTB), a Birnin Kebbi, da niyyar yin sata, wanda har ta kai an kulle banki da shi a ciki ya shiga hannu. An bayyana sunan wanda a ke zargi da Idam Jeremiah, inda ya yi yunkurin boyewa a cikin saman rufin bankin, sannan daga baya ya yi sata a cikin bankin.
Wani wanda lamnarin ya faru a gaban idanunsu ya bayyana cewa, matashin ya shiga bankin ne a matsayin abokin huldar bankin. “Lokacin da matashin ya shiga bankin a matsakin abokin huldar bankin, sai ya shiga bayi inda daga nan ne ya shiga cikin saman rufin bankin,” in ji shi.
An dai bayyana cewa, wata daga cikin masu sharan bankin ta ga takalmai da ya yi amfani da shi a cikin bayin wurin hawa saman rufin, ya nuna shaidar an hau saman rufin bankin. “Nan take ta sanar wa masu gadin bankin, inda daya daga cikin masu gadin ya hau saman rufin ya duba. A nan ne ya ga matashin labe a cikin saman rufin bankin,” in ji wata magiya.
An bayyana cewa, bayan an ga matashin a saman rufin bankin, sai manajan bankin ya kira ‘yan sanda, matashin ya ki fitowa daga saman rufin har sai da ‘yan sanda su ka yi masam barazanar idan bai fito ba, to za su harbe shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin. Ya ce, “a halin yanzu ana gudanar da binciken lamkarin.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: