Connect with us

RIGAR 'YANCI

Farfado Da Noman Auduga: Buhari Ya Cancanci Jinjina – Alhaji Sufyanu

Published

on

Duk wanda ke lura da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuduri farfado da noman auduga a daukacin Nijeriya ba jihohin Arewa kawai ba, ya san ya zama wajibi manoman auduga da kuma al’ummar Nijeriya su yaba wa shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar manoman Auduga a karamar hukumar zariya, Alhaji Sufyanu Abdullahi ya bayyana kalaman da suka gabata a lokacin da ya kammala jagorantar rarraba irin auduga da kuma takin zamani ga wadanda su ka kuduri aniyar shiga sahun bunkasa noman Auduga a karamar hukumar Zariya.

Alhaji Sufyanu Abdullahi ya ci gaba da cewar, zuwa lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, a kwai wadanda suka nuna shiga shirin bunkasa noman Auduga fiye da dubu hudu a karamar hukumar Zariya da suka hada da mata da suka fito daga daukacin gundumomin karamar hukumar Zariya goma sha uku.

Shugaban kungiyar manoman Auduga a karamar hukumar Zariya ya nunar da cewar, a kafin a tabbatar dab a duk mai sha’awar shiga tsarin bunkasa noman Auduga mace ko kuma na miji, ya ce sai da shugabannin wannan kungiya a karamar hukumar Zariya suka kafa wani kwamiti mai karfi, da aka dora ma sa alhakin ziyarar gonakin wadanda suka suka nuna sha’awarsu na shiga wannan tsari na farfado da noman Auduga.

Wannan kwamiti, kamar yadda Alhaji Sufyanu Abdullahi ya ce, mambobin kwamitin sun ziyarci manoman a gonakinsu, inda suka tabbatar da cewar, wadanda suka yunkura shiga wannan tsari cikakkun manoma ne da kuma su ka mallaki gonakin da za su yi noman Audugar, sai ya ce, dole ya jinjina wa mambobin wannan kwamiti, na yadda suka gudanar da ayyukan da aka dora ma su.

A game da matsalar yadda wasu manoma ke sayar da kayayyakin da a ka ba su, domin bunkasa noma a wasu tsare – tsaren da gwamnatin tarayya ta sa wa gaba, baya ga bunkasa noman Auduga, Alhaji Sufyanu ya tabbatar da cewar, tun daga ranar da suka fara bayar da irn Auduga ga manoman a kwai kwamitin asiri tare da sa ido da shugabannin wannan kungiya suka kafa, da aka dora ma sa alhakin ganin ba wani da aka ba shi irin Auduga ko kuma taki da sauran kayayyaki a karkashin wannan kungiya da ya yunkura domin sayarwa ga ma su shirin kawo nakasu a wannan tsari da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito da shi, domin dawo da matabatar noman Auduga a sassan Nijeriya.

Shi ma wannan kwamiti, kamar yadda Alhaji Sufyanu ya ce, sun yi aikin da dora su a kai, tun da ba a sami wani day a yunkura domin sayar da daya daga cikin kayayyakin da aka ba shi ba.

Sai dai kuma shugaban kungiyar ma su noman Auduga a karamar hukumar Zariya, Alhaji Sufyanu Abdullahi, ya nuna matukar damuwarsa na yadda babu yunkuri da gwamnatin jihar Kaduna ta yin a ganin ta yi koyi da shugaban kasa na batun bunkasa noman Auduga a jihar, baya gab a manoma wasu filaye a dajin da shigarsa a wannan lokaci na kamfar tsaro, babbar matsala ce.

A kan haka ne shugaban ya yi amfani da wannan dama, na yin kira ga gwamnonin arewa, da a jihohinsu su fara cika alkawarin farfado da masakun da suka durkushe, wanda zai tallafa wa manoman Auduga, da zarar sun kammala noman Audugar su doshi wadannan kamfanonin gurzar auduga da kuma masaku, domin burin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika, na dawo da martabar noman Auduga a Nijeriya.

A karshen ganawar da wakilinmu ya yi da Alhaji Sufyanu Abdullahi, ya yi addu’a ta musamman ga shugaban kungiyar manoman Auduga a jihar Kaduna Alhaji Mamuda Wapa, na rashin lafiyar da ya keciki.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: