Connect with us

WASANNI

Manchester United Ta Yi Wa Chelsea Cin Fin Karfi

Published

on

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya ci kwallaye biyu yayin da kungiyar ta sa ta lallasa Chelsea da ci 4-0 a gasar Firimiyar Ingila na farko a kakar wasa ta bana da ta fara da kafar dama a ranar Lahadi. Dama ‘yan wasan na Ole Gunnar Solskjaer na neman abin da zai huce musu takaici sakamakon munanan sakamakon da suka samu a kakar da ta gabata.

Rashford ya fara ci wa Manchester United kwallo ne a wasan daga bugun daga  kai sai mai tsaron gida, kafin daga bisani kwallaye uku suka samu bayan hutun rabin lokaci cikin mintuna 16 ta hannun Anthony Martial, Rashford, da sabon dan wasa Daniel James.

Su ma sabbin ‘yan wasan baya na Manchester United, Harry Maguire da Aaron Wan-Bissaka sun baiwa mara da kunya a wasan, lamarin da ya sa ake ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu, duk da cewa an kashe fam miliyan 130 wajen sayen su biyu.

Wannan ne wasan farko da sabon mai horas da Chelsea Frank Lampard ya jagoranci kungiyar a matsayin mai horarwa, inda ya yi karfin hali wajen farawa da matasa kamar Tammy Abraham da Mason Mount.

Baya ga dakatar da Chelsea daga sayen ‘yan wasa a kasuwan cinikin ‘yan wasa na wannan kaka, akasarin manyan masu murza tamaula a kungiyar suna fama da rauni, amma Lampard bai kawo hakan a matsayin hujja ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: