Connect with us

MAKALAR YAU

Tsakanin Arewa Da Makomar Kannywood

Published

on

Na san masu bibiyar wannan shafin za su yi mamaki matuka ganin taken da na yi wa makalar yau, musamman irin yadda al’umma a ke yi wa masana’antar Kannywood ta masu shirya fifanfinan Hausa wani irin kallo tsawon lokaci. Ko da ya ke, batun ba wai kawai ga al’ummar ba ne, ya shafi tsarin tafiya da gudanar da harkokin finafinai ta fuskar zamantakewa, siyasa da tattalin arziki. Ba lallai ne ra’ayina ya dace da maudhu’in da zan tattaunawa a kai ba, illa iyaka, tsinkaye da kuma laluben makomar Kannywood da a yanzu gidan kowa da akwai ta.
Wasu ka iya tambayar me ya kawo batun cewa gidan kowa da akwai? Sai dai wannan magana haka ta ke, idan mu ka yi la’akari da dubban mutanen da ke cin abinci a cikin harkar da kuma milyoyin mutanen da su ke kallon finafinan. Wadanda su ke cin abinci sun fara tun daga kan jarumai, masu shiryawa da bada umarni da kuma masu harkokin kasuwanci ta fanni daban-daban. Halin da a ke ciki a Arewa, babu wani gida da za ce ‘ya’yan cikinsa babu wanda ya ke kallon fim din Hausa.
Wannan abu ne mai matukar wahala ko ma a ce ba zai yiwu ba. Kididdiga ta nuna akalla sama da mutum miliyan 100 su na kallon finafinan Hausa ta hanyoyi daban-daban; ko dai ta kaset, faifai, gidan talabijin ko yanar gizo. Tarihin masana’antar da ya faro tun wuraren shekaru 30 da su ka shude, mutane da yawan sun yi kokarin dora ta kan gwadabe mai kyau ta yadda sana’ar za ta amfani al’umma da su kansu ‘yan fim din.
An yi rubuce-rubuce da taruka masu yawa kan wannan masana’anta tun a tsakanin shekarun 1998 zuwa 2000, wanda hakan shi ya haifar da hukuma ta musamman da za ta rika tace harkokin finafinan kafin su kai ga fita kasuwa. A wancan lokacin, hanyoyi kasuwancin finafinai biyu ne kacal, sinimu da ke birni da kewaye a garuruwa musamman Kano da Jos, sai kuma kaset da a ke kai wa kasuwa.
Ayyukan Hukumar tace finafinai a a lokacin ya takaita ne kawai kan kula da da’ar masu shirya finafinan ta yadda za su dace da addini da al’ada. Tabbas hakan ya taimaka kwarai da gaske wajen dakile barna, shirme da shiririta. A hankali duniya ta na canjawa, saboda haka zamani ya na kara shigo, komai na rayuwa ya na cigaba da daukar sabon salo. Harkokin hukumar tace finafinai, musamman ta Kano, ya tashi daga duba tsaftar finafinai kadai, har ya fara shiga harkokin mu’amala da cinikiyyar fim.
Har ila yau, tasirin da siyasa ta yi a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum, ya janyo hatta mukaman da a ke nadawa domin jagorancin hukumar siyasar ta na yin tasiri. Misali, zamanin tsohon gwamna Injiniya (Dakta) Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a lokacin ne a ka kafa hukumar, shugabanta ya na cikin manyan yara ko kuma magoya bayan Kwankwaso. A zahiri, ba shi da wata alaka ta sosai da masu shirya finafinai, illa iyaka Kwankwason ya amince zai iya gudanar da aiki yadda ya kamata. Ko da ya na da nasa kuskuren, amma ya taimaka sosai wajen bada shawarwari kan yadda za a gudanar da harkar fim ba tare da kauce hanya ba.
Zuwan Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a shekarar 2003 ya sauya akalar masana’antar Kannywood bakidaya, kasancewarsa gwamna da a ke yi ma sa kallo mai tsattsauran ra’ayin addini. Mutumin da ya nada a zamaninsa domin jagorantar Hukuma Tace Finafina Da Dab’i, wato Abubakar Rabo, ‘yan fim na yi ma sa kallon matsangwami, wanda ya hana su rawar gaban hantsi.
Ta bayyana karara irin rigingimu da bahallatsar da ta rika shiga tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin masana’antar. Wasu da dama hakan ya yi sanadiyar tafiyarsu gidan kaso, yayin da wasu ba shiri su ka hijira daga Kano, cibiyar kasuwancin finafinai, su ka koma wasu wuraren. Babbar matsalar da Kannywood ta fuskanta ta bangaren bunkasar harkokin kasuwanci ya fara ne daga wannan lokacin, ta kai shirya fim din kansa sai da ya gagari kowa, domin idan ka shirya ma babu kasuwar da za a kai.
Hukumomin sun tarwatsa kowa kokarinsu na saita al’amura (a ganinsu). Maimaikon a yi gyara, sai lamarin ya koma barna. Maimakon janyo ‘yan fim din jiki, sai a ka rika yi mu su barazana da dauri, hakan ta sa wasu su ka fice daga Kano, kuma ba su fasa shirya finafinan ba, wanda duk irin matakan tsaron da za a saka, sai finafinan sun shigo Kano ta barauniyar hanya, hukuma kuma ba ta da hurumin kama wani, tunda iya Kano kadai ta ke aiki. Allah ya albarkaci jihar Kano da abubuwa masu tarin yawa wadanda sauran jihohin su ke kwaikwayo. Fim na daga ciki.
Mutane da yawa sun bar garuruwansu na haihuwa su ka dawo Kano da zama. Hakan a zahiri ya na taimakawa kwarai wajen sama wa ‘yan Najeriya ayyukan yi. Mutane da yawa sun samu miliyoyin Naira, sun gina gidaje, sun zuba kudi a harkokin kasuwanci daban-daban, wanda haka ke taimakawa gwamnati matuka da gaske wajen rage ma ta nauyin dimbin matasa marasa ayyukan yi. Wannan dalili ya sa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya ba wa masana’antar muhimmanci a mulkin karo na biyu.
Ya kira ‘yan fim da su ka yi gudun hijira su dawo don cigaba da harkokinsu. Tsawon shekaru hudu na mulkinsa, harkar fim ta bunkasa, darajarta ta karu. Babu wani mutum da zai ci mutunci ‘yan fim, ya zauna lafiya. A shekarar 2015, sabuwar gwamnati karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa ‘yan fim tagomashin da babu gwamnatin da ta yi mu su, inda ta dauki dan cikinta, ta ba shi mukamin jagorancin hukumar tace finafinan, lamarin da ya yi kama da namu-ya-samu.
‘Yan fim din sun yi farin ciki matuka da wannan cigaba, kusan kowa ya rungumi tafiya da kuma tsari mai taken canji da sabon shugaban hukumar ya bullo da shi. Sai dai kuma jim kadan bayan hakan, sai kasuwar Kofar Wambai, wadda nan ne cibiyar hada-hadar finafinan Hausa ta fara gamuwa da tasgaro a lokacin da masu sana’ar cajin waya su ka gane tura fim a wayoyin hannu da kuma satar fasaha.
An yi asara ta miliyoyin Naira ta dalilin hakan. Duk da cewa hukuma ta yi kokarin dakile matsalar, amma a zahiri ta gaza ko ma a ce ta sake rura wutar matsalar ta hanyar yiwa masu waccan satar fasahar rijista, wato ’yan dowunlodin, lamarin da ya sanya wasu hakura da sana’ar ta fim kwata-kwata.
Masu taurin zuciya su ne su ka cigaba da jalautawa su na yin fim din, sannan su bi sahun masu satar fasaha domin kama su. Wannan ya janyowa ‘yan fim yin tafiyetafiye zuwa garuruwa domin nema wa kansu mafita. A irin wannan yanayi wasu ke yin hatsari a hanya su rasa ransu.
Tuni babbar kasuwar Kofar Wambai ta mutu murus, masu sana’ar kayan sawa su ka mamaye ta, kuma duk da haka hukuma ba ta fasa yi wa ‘yan fim barazana da dauri ba, domin wasu da yawa sun gamu da fushin hukuma da ya yi sanadiyar zuwansu gidan yari. Fim dai babbar sana’a ce ta so a Najeriya tun shekaru da dama da su ka gabata.
Yankin Arewaci da Kudanci sun karbe ta a matsayin wani jigo na rayuwarsu. Sai dai, ta fuskar kasuwanci da cigaba, tuni yankin Kudu su ka yi wa Arewa nisa. Yayin da bangaren Nollywood ke samun biliyoyi saboda irin gudunmawa da goyon bayan da su ke samu daga hukumomi, harkar fim a Arewa ta na yin cigaban mai haka rijiya ne. Matasa na tururuwar shigowa, su kuma hukumomi sun gaza wajen samar da bigire mai kyai na bunkasa masana’antar.
A nawa nazari da ra’ayin, Kannywood ba tsangwama da barazana ta ke bukata ba, illa tsari mai kyau ta hanyar nuna soyayya da kauna. Yanzu ba lokaci ne na koma wa tsarin shekarun baya – na kamu da dauri – ba. Mu na 2019 yanzu, wanda saura wata hudu kacal mu shiga 2020.
Duniya ta dade da karbar tsarin cigaba fasahar zamani, amma Kannywood da masu ruwa da tsakinta sun gaza bullo da tsari wanda a shekaru daruruwa masu zuwa mutane za su amfana. Ko da ya ke, an samu bayyanar Manhajar Northflid da kuma irin kokarin da a yanzu haka mutane irin su Dakta Ahmad Sarari ke yi na samar da gidan talabijin na musamman da zai rika nuna finafinan Kannywood kadai.
Haka nan a yankin jihohin Zamfara da Sokoto an samu Alhaji Sani Rainbow, wanda ya ke kokarin kafa gidajen kallo a jihohin. Tabbas irin wadannan labarai su ne labaran da Kannywood din ke bukatar ji da gani, ba batun dauri da kai mutane gidan yari ba. Northflid Manhaja ce da a ka kashe miliyoyin kudi wajen samar da ita ta yadda a yanzu ta zama madogara ta cigaban kasuwancin finafinan Hausa, domin al’umma Hausawa mazauna kasashen waje su na da damar kallon finafinan a duk lokacin da su ke bukata.
Kannywood TB kuwa da Ahmad Sarari ke kokarin samarwa, da zarar ta fara aiki, dubun-dubatar matasa da su ka yi karatu a fannoni daban-daban na rayuwa za su iya aiki tare da ita, a hannu guda an ragewa gwamnati nauyin kula da ayyukan matasa. Haka nan wadanda gidajen kallo na zamani da Alhaji Sani ke samarwa a Zamfara da Sokoto su ma za su taimaka wajen samar da aikin yi, wanda hakan zai iya rage matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Babban abin tsoron shi ne, salon takun da hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta zo da shi a zangonta na biyu, inda bayan sake nada da Babban Sakataren hukumar, Isma’il Na’abba Afakallahu, a ka ruwaito shi ya na yin barazana ga masu sana’ar ta hanyar yi mu su kashedi da kamu da dauri a gidan kurkuku, sannan kuma a ka sake ruwaito shi ya na ganawa da alkalai guda uku, wadanda hukumar za ta hada kai da su wajen daure masu sana’ar shirin fim a jihar.
Wannan al’amarin fa ya na faruwa ne a lokacin da wasu jihohi da kuma daidaikun mutane ke kokarin yin amfani da wannan baiwa da allah ya yi wa Arewa ta masu fasaha wajen samar da aikin yi a Kannywood. Duk yadda mu ke kokarin wayar da kan al’umma wajen bin doka, amma dauri da kai wa gidan yari ba shi ne mafita ga mutanen da su ke sana’a ba.
Tallafi su ke bukata na bunkasa masana’antarsu a daidai wannan lokaci. Gudunmawa su ke bukata daga wurin hukumomi ta kowane yanayi. Idan har wasu na waje na yunkurin shigowa su zuba hannun jari, irin wadannan kalamai za su razana su, su koma wani bangaren don zuba kudadensu. Misali, mu kalli jihohin Borno da Zamfara, gwamnati kokari ce ta ke fito da mutane daga gidan yari, ta na koya mu su sana’o’i, domin su dawo rayuwa cikin mutane, duk da cewa sun aikata manyan laifuka na tada hankali da kisan jama’a.
Hatta ’yan ta’adda ma gwamnati ta na kokarin saka su a tsarinta na yafiya ne tare da ba su aikin yi. To, me ya sa jihar Kano za ta rika daure matasan da su ka samar wa da kansu aikin yi, su ka bijerewa ayyukan ta’addanci? Shin a na so ne nan gaba su fantsama waccan mummunar sana’a ne, saboda barazana ta yi mu su yawa? Wannan zai nuna ma na cewar ita gwamnati a koda yaushe, ba wai dauri da kamun ta ke so ba, ta fi so mutane su rayu cikin yarda da aminci.
Ashe kenan, kamu da dauri ba shi ke ganin matsala ba, janyo mutane jiki a mu’amalance su shi ne mafita. Kannywood dai masana’anta ce da ta ke samun gindin zama ba Arewa kadai ba, Najeriya bakidaya. Idan Hausawa su ka daina yin fim, to tabbas Yarabawa da sauran manyan kabilun Najeriya za su karbi sana’ar su rika yi ta yadda al’ummarmu ba za su iya hana su yin abinda su ka ga dama ba. Arewa na bukatar masana’anta irin Kannywood wajen bunkasa harkokin tattalin arziki.
Hakki ne yanzu a wurin gwamnati ta sake duba dokokin fim da a ka rubuta shekaru 20 da su ka gabata, tsarin rayuwarmu na yau da kullum ta kowace fuska sun canja, saboda haka daftarin ya na bukatar garambawul, domin ya dace daidai da zamani. Matsalar Kannywood guda daya ce a yanzu, Kasuwanci, gwamnati ta yi tsari, ta duba yiwuwar tallafawa masana’antar da a lokacin zabuka ke bawa ‘yan siyasa gudunmawa idan za a ce kamfen.
Maganar kamu da daure mutane ba za ta haifar Kano da gwamnatin Kano da mai ido ba, domin daga lokacin da wasu su ka balle tabbas shawo kansu zai yi matukar wahala. Ba koda yaushe ne barazana da kokarin daure mutane ke maganin matsala ba, a na bukatar tsarin diflomasiyya wajen gudanar da wasu abubuwan.
Mai girman Gwamnan Jihar Kano, wanda ya ba wa masana’antar Kannywood gudunmawa daidai bakin gwargwado, shi ne mutum daya tilo da a yanzu zai magance kalubalen da ‘yan fim ke shirin fuskanta, hukumar ta ce ta mayar da hankali wajen bunkasa Kannywood ta fuskar cigaban kasuwanci ba dauri ba. Tarihi ya na da dadi, a na bada shi ne, domin mutane su koyi abinda a ka yi ko su kauce masa, don gudun fada wa fitina.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!