Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Islamiyyar Al-Irshadiya Ta Matan Aure Ta Bunkasa A Mile 12

Published

on

Ilimin karatun Arabiya kai har da ma na zamani su na da matukar mahimmanci a wajen matan aure, domin koya wa ’ya’yansu mata tarbiyya tagari da kuma halin zamantakewar da ke tsakanin miji da matarsa a gidajen aurensu. A kan haka ne ya sanya Hajiya Maryam, matar Alhaji Dayyabu, da ke kan titin Alshatu Street a unguwar Mile 12 da ke Legas ta bude makarantar isilamiya, domin koya wa matan aure ilimin karatun Arabiya, wanda za su yi amfani da shi a gidajen mazajen aurensu har ma aka kai ga yaye wasu daga cikin daliban makarantar.

Taron yaye daliban, wanda ya gudana a harabar makarantar da ke umguwar Mile 12 a ranar Lahadin da ta gabata, makarantar ta kasance ita ce ta farko wacce matan aure su ke koyar da mata ’yan uwansu karatun addinin Musulunci a yankin, sannan kuma taron yaye daliban ya samu halartar matan manyan Hausawa da matan manyan malamai da Yarabawa da sauran kabilu Musulmi mazauna unguwar ta Mile 12.

A jawabinta na babbar bakuwa a wajen taron, uwargidan shugaban kasuwar ta Mile 12, Hajiya Musulmat Alhaji Shehu Usman Sampam, ta yi fatan alheri ga wadannan mata da Allah ubangiji ya ba su damar sauke karatun Alkur’ani mai tsarki a daidai wan nan lokaci, sannan kuma ta umarce su da su cigaba da gudanar da wannan karatu na isilamiya tare da yin amfani da ilimin da su ka koya a gidajen mazan aurensu da sauran al’amaran da su ka shafi rayuwarsu da halin zamantakewar al’umma bakidaya. Yayin da ta ke mayar da nata jawabin ga matan aure ’yan uwanta, shugabar makarantar ta Al-irshadiya Isilamiya a wajen walimar yaye daliban Hajiya Maryam Dayyabu bayan ta kammala isar da sakon godiyarta ga Allah Ubangiji Madaukakin Sarki mai kowa mai komai da ya ba ta damar bude wannan makaranta.

A cewarta, tun daga shekaru 15 da su ka wuce da ta bude wannan makaranta zuwa yanzu makarantar ta samu cigaba bila’adadin tunda an bude makarantar ne da dalibai shida zuwa bakwai, amma yanzu ta na da dalibai matan aure 70 zuwa 80. Kuma wannan walimar ita ce karo na farko a wajen yaye dalibai da wannan makarantar ta yi a wan nan shekarar.

Sannan ta cigaba da umartar masu hannu da shuni da sauran attajirai da su cigaba da tallafa wa wannan makaranta, domin kwalliya ta kara biyan kudin subulu. A jawabinta na nuna jin dadi, mataimakiyar sakatariyar wannan makaranta, Hajiya Hadiza Abubakar Paki, matar Alhaji Habu Paki, ta nuna farin cikinta ne a game da daukakar da Allah ya yiwa wannan makaranta tare da samun kwararrun mata malamai wadanda su ke koya wa matan auren wannan unguwar ta Mile 12 karatun addinin Musulunci.

Bayan kammala jawabin mataimakiyar sakatariya wannan makaranta ne, Hajiya Hadiza Abubakar Paki uwargidan Alhaji Habu Paki, a ka umarci daliban da su karanto wadansu ayoyi a cikin Alkur’ani mai tsarki kuma su ka karanto bakin abinda ya sauwaka. Sannan hukumar makarantar a karkashin jagorancin shugaban makarantar Hajiya Maryam Dayyabu ta ba wa wadannan dalibai takardar shahada ta shaidar saukar wannan karatu, sannan a ka rufe taro da addu’a.

To, bayan kammala taron walimar ne duk da ya ke hidima ce ta mata, sai mu ka ga yakamata a ji ta bakin wadansu daga cikin mazajen wadannan dalibai matan aure da wannan makaranta ta yaye su a wannan lokaci. Alhaji Habu Paki ya na daya daga cikin masu mata a cikin wannan maranta. Ya ce, lallai ya na cikin farin ciki a game da samun wannan makaranta ta matan aure mai dauke da dumbin tarihi, wacce ita ce ta farko da a ka samu da malamanta da daliban cikin makarantar duk kansu matane babu na miji ko daya, sannan kuma makarantar Allah ya ba ta hazikan malamai mata masu zurfin ilimin karatun islamiyya da sauran makaman tansu, in ji shi, ya ce, ya na farin ciki da wannan al’amari, sannan ya umarci attajirai da su cigaba da tallafa wa wannan makaranta a wajan samun matsuguni na zaman dindindin.

Alhaji Ubale babu munafunci kasuwar Mile 12 shi ma daya ne daga cikin masu mata a wannan makaranta kuma ya cigaba da tsokaci kamar haka ya ce farko dai ya na taya mazajen wadannan mata dalibai da su ka sauka na wannan makaranta, sannan kuma ya ce ya na kira ga sauran al’umar mazauna kasuwar Mile 12 da su cigaba da ba wannan makaranta hadin kai da goyon baya tare da sanya matansu cikin wannan makaranta, domin su koyi ilimin addinin Musulunci Alhaji Muntari Jabo, wanda shi ne shugaban kwamitin masallacin juma’a a na ’yan darika a kasuwar Mile 12.

Ya cigaba da nuna farin cikinsa ne a game da samun wannan makaranta ta matan aure, in ji shi, wacce malamanta da daliban ta duka mata ne kuma ta ke dauke da malamai mata masu zurfin ilimin addinin Musulunci, sai ya ce, ya na yiwa dukkan Musulmin Mile 12 fatan alheri a game da wannan babban abin farin ciki a wannan unguwar ta Mile 12.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: