Connect with us

LABARAI

Bayan Shekara Biyar… Karon Farko An Yi Bikin Sallah A Bama

Published

on

Al’ummar garin Bama da ke jihar Borno sun samu sakata da walawa a karon farko bayan shekara biyar, inda su ka samu ikon gudanar biki Babbar Sallah a masarautar tasu, bayan da sojojin Najeriya su ka rage kaifin tasirin kungiyar Boko Haram a yankin.

Mai martaba Shehun Bama a jihar Borno, Mai Kyari Ibn Umar El-Kanemi, ya tabbatar da cewa, wannan shi ne karon farko a cikin shekara biyar, inda a cikin jama’ar masarautar su ka gudanar da bikin babbar sallah cikin aminci tare da sauran al’ummar Musulmin duniya.

“Yau sai ga shi mu na gudanar da shagulgulan babbar sallah a garin Bama; abinda ya gagare mu shekara biyar da su ka gabata. Bisa ga wannan ne mu ke mika dimbin godiyarmu ga Allah madaukakin sarki, da ya ba mu tsawon rai tare da ganin wannan rana a garin Bama.”

Garin Bama ya na daga cikin garuruwa a jihar Borno wadanda su ka sha fuskantar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram, kana su ka tilasta wa Sarkin na Bama tare da sauran al’ummar garin kaura zuwa birnin Maiduguri.

A baya dai, rahotani sun nuna yadda mayakan kungiyar Boko Haram su ka taba yin garkuwa da matar Shehun na Bama, Umar El-Kanemi, tare da ’yarsa a 2014, wadanda a ka sako su bayan shekaru biyu.

Sarkin Bama tare da takwaransa na Dikwa, Mai Masa Ibn Umar El Kanemi, sun koma da zama a babban birnin jihar, Maiduguri, da jama’arsu ne.

Shaidun gani da ido sun bayyana yadda jama’a ke cigaba da kai-komo cikin yanci a garin Bama ba tare da wani kace-nace ko fargaba ba, kuma an gudanar da sallar ba tare da wani kalubalen kai harin Boko Haram ba.

Haka zalika kuma, an gudanar da gangamin addu’o’i na musamman a ranar Lahadi, saboda murnar dawowar Sarkin na Bama a garin bayan dogon lokaci ba ya nan.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: