Connect with us

Uncategorized

Miyati Allah Ta Jinjiwa Gwamna Matawale Kan Wasan Fulani A Zamfara

Published

on

Wasan Sallah Fulani a Zamfara kungiyar miyati Allah ta jinjina wa Gwamna Bello Muhammad  Matawale da ya jagorancin gagarimin bikin Sallah da ba a tabayinsa ba kasar nan.

Uban kungiyar Miyati Allah na Jihar Alhaji Ahmad Hussaini Matawalen Tudun wada ne ya bayyana jinjinar a lokacin da ake gudanar wasan sallah wanda ya kunshi harda sharo a Gusau Baban birnin jihar Zamfara.

Alhaji Ahmad Matawalen Tudun ya kuma bayyana cewa’ wannan wasan sallah daga koina ya samu karbowa kuma ya kara hada zumuncin filanin arewacin kasar nan ,dan dubannan Fulani ne suka larci wannan wasan.kuma wasan ya kara mana hadin kai da kuma tabbacin zaman lafiya zai dore a jihar Zamfara da kasa baki daya da yardar Allah.

Matawalen Tudun Wada yayi kira ga Gwamnonin kasar nan da suyi koyi da Gwamna Bello Muhammad Matawale wajan hadin kan alummar su .da kare rayukan su da cigaban su.kuma muna rokon Allah da ya cikawa Gwamna Matawale kudirin sa na cigaban jiahr mu da kasa baki daya.

A nasa jawabin Gwamna Bello Muhammad Matawale, ya mika gidiyar sa ga Allah da Kuma Fulani da sukai wa jihar Zamfara fitar Farin dango kwansu da kwarkatar su suka shigo Gusau dan yin wannan gagarimin biki.

Kuma a nan take Gwamna Matawale ya ba Shugabanni  kananan hukumomin umarni yin wannan biki a cikin kananan hukumomin su.

Gwamna Matawale ya tabbatar da kudirin sa na Gina Rugage da Asjbitoci  da makarantu dan jin dadin su da walwalar su.a gadin jihar ta zamfara
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: