Connect with us

WASANNI

Omeruo Ya Koma Legannes Daga Chelsea

Published

on

Dan wasan baya na tawagar Super Eagles, Kenneth Omeruo ya koma kungiyar kwallon kafa ta Legannes wadda take buga gasar laliga ta kasar Sipaniya bayan da dan wasan yayi zaman aro a kungiyar a kakar wasan data gabata.

Dan wasan bayan dai ya buga wasanni 31 a kungiyar a kakar wasan data gabata duk da cewa zaman aro yayi kuma acikin wasannin daya buga, wasanni 30 duka dashi aka fara wasan hakan yana nufin baiyi zaman benci ba tun daya koma kungiyar.

A satin daya gabata ne dai kungiyar ta Legannes ta fara tattaunawa da Chelsea akan dan wasan yayinda Chelsea ta bukaci fam miliyan 6 ita kuma Legannes tace fam miliyan 4 zata iya bayarwa akan dan wasan mai shekara 25 a duniya.

Dan wasan dai ya koma Chelsea ne a shekara ta 2012 daga kungiyar Atandard Liege ta kasar Belgium kuma Chelsea ta kaishi kungiyoyi da dama yayi zaman aro irin su kungiyar kwallon kafa ta ADO Den Haag dake kasar Holland da Middlesbrough ta kasar Ingila sai kuma Kasimpasa da Alyanporo duka a kasar Turkiyya kafin kuma yaje Legannes yayi zaman aro na shekara daya.

“Ina ganin yanzu lokaci yayi da zan samu kungiya guda daya in zauna sosai domin fuskantar inda yakamata in saka a gaba saboda yanzu shekara ta 25 kuma inada aure da yarinya guda daya saboda haka bai kamata in dunga yawo kasa kasa ba” in ji Omeruo, wanda yana bugawa Super Eagles wasa

Ya cigaba da cewa “Chelsea tayi min duk abinda yakamata a matsayina na dan wasan kungiyar saboda haka ina godiya da irin yadda kungiyar ta rike ni sai dai nima yanzu ina bukatar zama a waje daya”

‘Yan wasa irinsu Bakayoko da Kennedy da kuma Zapacosta sune ‘yan wasan da ake ganin zasu bar Chelsea kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bana duk da cewa an hana kungiyar sayan ‘yan wasa amma tana cigaba da rabuwa da wasu daga cikin ‘yan wasanta.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: