Connect with us

RA'AYINMU

Batun Cibiyar Warkar Da Masu Tabin-Hankali Da Maganin Gargajiya

Published

on

Nijeriya na daya daga cikin kasashen da suka yi suna wajen amfani da magungunan gargajiya da kuma cibiyoyin warkar da masu tabin hankali a gargajiyance, kamar yadda al’ummar Chana su ma suke da nasu salon magungunan gargajiyar, musamman ta fuskar yin amfani da zare da allura wajen yin tiyata tare da warkar da masu tabin hankali ta yin amfani da irin magungunansu na gargajiya.

Duk inda ka kewaya a Nijeriya babu inda ba za ka samu masu bayar da magungunan gargajiya ba, haka nan cibiyoyin warkar da masu tabin hankali wadanda su ne ke kankane da masu dauke da irin wannan lalura ba sa kuma son a rika amfani da na Asibiti. Amma saboda wasu abubuwa da wasunsu kan yi amfani da su masu kama da tsafi ko wani abu makamancin haka a wajen bayar da magungunan nasu, ya sa wasu lokutan ba a fiye ba su muhimmanci ba.

A wannan mako dai, wannan Gidan Jarida ya mayar da hankali ne a kan wata Cibiya ta warkar da masu tabin hankali mai suna Musabil Herbal Centre, da ke garin Gauta, Keffi Dan Yamusa a Karamar Hukumar Keffi da ke Jihar Nassara, inda a halin yanzu muke samun labarin cewa sun warkar da masu tabin hankalli su kimanin 47a wannan Cibiya.

Har ila yau, Cibiyar na ci gaba da ikrarin cewa, tana dab da sake warkar da wasu masu tabin hankalin 103. Sannan akwai maza guda 40 da aka tara su a cikin daki guda daya tak. Wadannan masu tabin hankali dai, guda 70 maza ne, 33 kuma mata.

Haka zalika, babban abin birgewa kuma shi ne, dukkanin wadannan masu tabin hankali, babu ko guda daga cikin su ke daure kamar yadda aka saba gani a Asibitoci da sauran Cibiyoyin warkar da masu tabin hankalin na gargajiya. Bugu da kari, shi ne yadda masu tabin hankalin ke gudanar da mu’amala a tsakaninsu duk da cewa suna zaune a daki guda da kuma yadda suke sake wa iyalansu da sauran masu kawo musu ziyara wurin da ake yi musu wannan magani.

Kazalika, masu bayar da wannan magani da sauran wadanda suke zuwa ziyarar marasa lafiyar sun bayar da tabbacin cewa, tun da aka bude wannan Cibiya ko Asibiti, ba a taba samun wata hayaniya ko hargitsi a tsakanin wadannan masu tabin hankali ba. Shugaban wannan Cibiya, wanda ake kira Darakta Janar, Dakta Kabiru Mohammad, wanda aka fi sani da Dakta Naborgu, ya bayyana cewa, wannan Cibiya an kafa ta ne watanni goma sha biyar da suka wuce.

Wannan dan asalin Fakachi ta Kainji, da ke Karamar Hukumar Borgu na Jihar Neja, wanda ya koma Jihar Nassarawa da zama, ya bayyana cewa ya gaji wannan sana’a ta warkar da masu tabin hankali ne daga wurin Mahaifinsa.

Haka nan, Daktan ya sake bayyana cewa, yawan masu tabin hankali da suka samu lafiya a hannunsa suna da yawa, amma guda 47 din da suka warke ya sallame su a cikin watanni 15, 20 daga cikin su suna nan tare da shi ya ba su aikin kula tare da yin gadi yana kuma biyan su albashi.

A wannan Asibiti ko Cibiya, akwai bangare daban-daban da ya hada da na maza da mata; sannan akwai likitoci daga bangare daban-daban shi ma da suke yin aiki tare da Mohammed, sai dai da magungunan gargajiya kadai suke yin amfani. Duk dai da cewa, Asibitin ba za a ce ya wadatu ko tsarinsa ya yi yadda ake so ba, amma ya kyautu Gwamnatin Jihar Nassara ta shigo ciki ta ba da nata gudunmawar don kyautatuwar al’amuran.

A namu bangaren, muna baiwa Jami’an Hukumar lafiya ta wannan Jiha, da su mayar da hankali wajen bibiyar abin da wannan Cibiya ke ciki musamman ta fuskar kyautata muhallin da wadannan masu tabin hankali ke karbar magani, tare da tabbatar da ganin cewa an inganta shi. Misali, Gwamnati za ta iya yin amfani da wannan dama wajen rage yawan cinkoson wadannan marasa lafiya, musamman ma maza. Idan muka dubi yadda ake hada masu tabin hankali su 40 a daki guda, babu tabbacin samun cikakkiyar tsafta da kuma ita kanta lafiyar jiki.

Kazalika, Gwamnatin Jiha ta yi watsi da barazanar cewa, za ta rufe wannan Cibiya duk kuwa da irin matsi da takura da za a yi mata, musamman daga wajen Sarakunan Gargajiya da Shugabannin addini, wadanda ke tsoratarwa a kan Asibitocin gargajiya, maimakon yin bincike a gano ko suna wata illa ko babu.

Don haka, yana da matukar muhimmanci mu rika yin watsi da ire-iren tunaninmu na cewa, duk wani magani da ke da alaka da na gargajiya a Nijeriya, shirme ne ba kuma a taba daukarsa da muhimmanci. Lokaci ya yi da ya kamata mu yi koyi da Kasar Chana, wadanda a halin yanzu suke iya sarrafa magungunansu na gargajiya suna fitar da su sauran Kasashen duniya suna sayarwa.

Saboda haka, lokaci ya yi da ya zama wajibi mu shiga hankalinmu, mu kuma yi amfani da zahiri ba mu tsaya muna yin suka a kan abubuwa masu amfani ba, don wata manufa ko wani ra’ayi namu na daban ba. Don haka, a halin yanzu babu abin da wannan Cibiya ta Musabil ke bukata da wuce ci gaba da ba ta kwarin gwiwa tare da sauran tallafi ba, don kuwa ko babu komai tana taimakawa wadannan masu tabin hankali su samu lafiya kamar yadda kowa kan iya zuwa ya bincika.

A karshe, muna kira ga Gwamnatin wannan Jiha, ta taimaka wa wannan Cibiya wajen samun cikakken horo wanda zai taimaka mata wajen ciyar da ita gaba, sannan a samar da wani yanayi wanda zai taimaka wa masu tabin hankalin da suka warke kafin su kai ga koma wa gidajensu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!