Connect with us

Uncategorized

Kano Pillars Ta Sayi ‘Yan WasaShida Kuma Ta Kori Guda Shida

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dake jihar Kano ta sayi ‘yan wasa shida wadanda kungiyar take ganin zasu taimaka mata domin tunkarar kakar wasa ta gaba kamar yadda mai Magana da yawun kungiyar ya bayyanawa manema labarai.

Rilwanu Idris Malikawa Garu, wanda kuma shine mai Magana da yawun kungiyar shine ya shaidawa manema labarai inda yace kungiyar, wadda ta kare kakar wasan data gabata a mataki na biyu ta samu damar sayan sababbin ‘yan wasa guda shida kuma ta sallami ‘yan wasa shida.

Har ila yau, Malikawa ya bayyana cewa tuni kungiyar ta kammala yiwa ‘yan wasan rijista a hukumar kwallon kafa ta kasa wadda hakkinta ne ta yi musu rijistar kuma sun shirya tsaf domin tunkarar kakar wasa ta gaba.

“Mun kara samun manya kuma zakakuran ‘yan wasa guda shida wadanda muke bukata kuma zasu taimaka mana a kakar wasa mai zuwa saboda haka mun gama shiryawa domin fara kakar wasa ta gaba da kuma gasar cin kofin zakarun nahiyar africa” in ji Malikawa

Sababbin ‘yan wasan da kungiyar ta saya sune; Abdullahi Musa, dan wasan baya daga kungiyar Wikki Tourist sai Nasiru Sani daga kungiyar Enyimba shima dan wasan baya sai kuma Stone Samuel daga kungiyar Go Round.

Ragowar sune Alaekwe Chijoeke, dan wasan gaba daga Efeanyi Uba sai Meshack Chukwubuike shima dan wasan gaba daga Yobe Desert sai kuma Usman Musa dan wasan gaba daga kungiyar Gombe United.

Har ila yau Kano Pillars din ta sallami ‘yan wasa guda shida wadanda take ganin bazasu taimakawa kungiyar ba ciki akwai Seun Akinyemi da shammah Tanze da kamal Sikiru da Danladi Isa da Hamza Abba Tiya.

Kano Pillars dai tana wakiltar kasar nan a gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa inda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko daci 3-2 yayinda a karshen wannan watan zasu kai ziyara kasar Ghana domin buga wasa na biyu sannan kuma a ranar 22 ga watanSatumba za’a fara sabuwar kakar wasa ta ajin firimiya kamar yadda hukumar kula da gasar ta bayyana.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: