Connect with us

KASASHEN WAJE

Harin Bom: IS Ta Dauki Alhakin Kashe Mutum 63 A Afghanistan

Published

on

Kungiyar IS ta dauki alhakin mummunan harin bom din da ya halaka mutum 63 tare da jikkata wasu 182 a wajen taron daurin aure a garin Kabul babban birnin kasar Afghanistan.

Kungiyar ta IS ta ce wani mayakinta ne ya tarwatsa bom din da ke jikinsa, yayin da ake tsaka da bikin, harin da hukumomin kasar suka ce shi ne mafi muni a baya-bayan nan. Harin ya zo ne a daidai lokacin da wakilan mayakan kungiyar Taliban da Amurka ke gab da cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin kusan shekara 18 da suke gwabzawa, matakin da zai bada damar janye dubban dakarun Amurkan dake kasar ta Afghanistan.

Tuni dai kungiyar Taliban ta nesanta kanta daga harin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: