Connect with us

LABARAI

Matar Gwamnan Jihar Kaduna Ta Fara Zagayen Godiya Ga Al’ummar Jihar

Published

on

A ci gaba da bayyana godiya ga al’ummar jihar dangane da nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a Kaduna, Mai Dakin Gwamnan, Hajiya Aisha (Ummi) Garba el-Rufai, kuma jagorar gangamin yakin neman zaben APC mai taken ‘APC Gida-Gida’ ta fara zagayen yi wa al’ummar jihar baki daya godiya da ban gajiyar zabe.

A cikin wata sanarwa da jami’ar yada labarai ta gangamin, Hajiya Jamila Farouk, cewa ta yi dalilin assasa zagayen shi ne domin yaba wa al’ummar jihar kan yadda suka jajirce wajen zaben Malam Nasir Ahmad el-Rufai a karo na biyu da kuma cika alkawarin da matar Gwamna ta yi mu su tun farkon farawa.

Da take kaddamar da shirin, matar gwamnan,  Hajiya Ummi el-Rufai ta ce babban dalilin assasa zagayen shi ne domin a yaba ma al’umma kan yadda suka dage suka jajirce wajen zaben Shugaba Muhammadu Buhari da Malam Nasir el-Rufai a karo na biyu, sannan kuma ta cika alkawarin da ta yi wa al’ummar jihar a yayin yakin neman zabe cewar da zarar sun yi nasara za ta dawo domin abin da masu hikima ke cewa, ‘Yaba kyauta tukwici.’

Ta ce, “Ina mai mika godiyar musamman ga dukkanin al’ummar jihar Kaduna kan yadda suka jajirce wajen sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari da Malam Nasir El-Rufai, domin su ci gaba da ayyukansu na alheri.  Haka kuma mun dawo gare ku ne domin mu cika alkawarin da muka yi mu ku a farko cewa da zarar mun yi nasara, za mu dawo godiya,” cewar matar gwamnan.

Sannan ta yaba wa al’ummar Igabi, wanda a nan ne ta fara yada zango na zagayen, inda ta ce mutanen Igabi sun yi kokari matuka, musamman ma ganin yadda suka goya wa Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Yusuf Ibrahim Zailani. A cewarta Hon Zailani daya ne daga cikin wadanda suke marawa gwamnatin Malam el-Rufai baya a jihat Kaduna.

Tun da fari dai, Hon. Zailani ya mika godiyar musamman ga matar gwamnan, sannan ta kara jinjinawa gwamna el-Rufai bisa kyawawan ayyukansa a fadin jihar, musamman a karamar hukumar Igabi.

Haka kuma ya yi wa Shugaba Buhari godiya kan yadda ya ba da mukaman minista guda biyu a Kaduna.

Tawagar dai ta yada zango a karamar hukumar Igabi, sannan za ta ci gaba a sauran kananan hukumomi na Jihar Kaduna.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: