Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Gurguwa’

Published

on

Suna: Gurguwa

Tsara Labari: Hafsat A. Ladan

Kamfani: Hausawa Movies

Shiryawa: Abdul Amart Umarni: Sadik N. Mafiya

Jarumai: Abdul M. Sharif, Maryam Yahya, Alhassan Kwalli, Malam Inuwa, Hajiya Aisha Yola, Ladidi Fagge, Abba El-Mustapha da sauransu.

A farkon fim din an nuna Salim (Abdul M. Sharif) yazo wajen budurwar sa Nafisa (Maryam Yahya) wadda larurar gurguntaka ta same ta bayan an  saka mata ranar aure da masoyin ta Salim. Salim ya sanar da Nafisa cewar ya fasa auren ta saboda larurar da ta same ta wadda yake ganin hakan bazai bashi damar nuna mata soyayyar da yake buri ba. Sai dai kuma bayan Salim yaje wajen mahaifin sa (Malam Inuwa) ya sanar masa da kudurin sa na janye auren Nafisa, sai mahaifin sa ya nuna sam bai amince a fasa auren ba.

Wannan dalilin ne yasa mahaifin Salim yazo wajen mahaifin Nafisa wato Alhaji Nafi’u (Alhassan Kwalli) ya tabbatar masa da cewar har a sannan dan sa Salim fa yana nan akan kudurin auren ‘yar su Nafisa. Jin hakan ne yasa Alhaji Nafi’u yayi godiya kuma yaje ya nuna wa Nafisa cewar ta kwantar da hankalin ta har yanzu maganar auren ta da Salim ba a janye ba. Shi kuwa Salim sai mahaifiyar sa (Ladidi Fagge) ta goyi da bayan sa akan sam bata amince dan ta ya auri gurguwa ba, jin hakan ne mahaifin Salim yayi mata barazana da zai saketa matukar bata cire hannun ta akan maganar ba. Tsoron abinda zai biyo baya ne yasa mahaifiyar Salim ta amince da auren sa da Nafisa. Sai dai kuma tun a ranar farko bayan Nafisa wadda aka daurawa aure da Salim ta tare a gidan sa sai ya soma bin ta da miyagun maganganu har da duka da bulala duk saboda ta aure sa, sannan yayi mata albishir da zama cikin kunci matukar bata gudu ta shiga duniya ba. Cikin dan lokaci kadan Nafisa ta soma fuskantar ukuba a zaman ta da Salim wanda tuni ya je wajen mahaifin sa akan yana son kara aure, haka kuwa aka yi ba a dau lokaci ba ya auri Safina (Bilkisu Shema) wadda akan idon ta yake gallazawa Nafisa idan kuma tayi laifi a gaban amaryar tasa yake dukan ta.

Cikin dan lokaci kadan Nafisa ta rame ta lalace, wata rana Hidaya kanwar Salim tazo gidan sa bayan dawowar ta daga karatu daga garin Gombe. Ganin halin da Nafisa ke ciki ne ta tausaya mata har ta tambaye ta silar nakasar da ta same ta ta gurguntaka. Anan ne Nafisa ta bata labarin tsohon saurayin ta (Abba El-Mustapha) wanda ya nuna mata soyayya amma ta wulakanta sa saboda tana soyayya da Salim. Da kuma dan kanwar mahaifin ta wanda shima yake son ta amma ta wulakanta sa har hakan ya zamo sanadin da zumuncin iyayen su ya ruguje. Bayan faruwar hakan ne ta wayi gari taga kafarta daya ta shanye.

Jin abinda ya faru ne yasa Hidaya ta shawarci mahaifin ta akan maganar wani malami da ta sani a jihar Gombe. Bayan zuwan su gidan malamin ne ya basu taimakon addu’o’i wanda cikin dan lokaci kadan Nafisa ta warke kafafun ta suka dawo daidai. A lokacin ne kuma Salim suka dawo shi da amaryar sa daga kasar waje tun bai fahimci cewa Nafisa ta warke ba ya sake ta. Sai dai kuma bayan ya sake ta ne mota ta buge shi kafafun sa suka lalace har aka yanke. A sannan ne yayi nadama bisa abinda ya aikata, yayin da amaryar sa Safina ta gujesa saboda ta nuna dama saboda kudin sa ta aure sa daga baya kuma ciwo ya cinye komai. Bayan ya saki Safina ne ya roki gafarar Nafisa, nan fa ta yafe masa tare da gabatar masa da mijin da zata aura.

Abubuwan Birgewa:

 • Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, kuma har ya dire bai karye ba.
 • Sauti ya fita radau, haka ma hoto babu makusa.
 • Jarumar sun yi kokari musamman Nafisa (Maryam Yahya) wadda taja fim din.
 • Daraktan fim din yayi kokari wajen ganin labarin ya tafi ta hanyar da ta dace. Haka ma me Camera yayi kokari wajen nuna salon aikin sa.
 • An samar da wuraren da suka dace da labarin.
 • Kalaman bakin jaruman wato (Dialogue) sun yi dadi da ma’ana.

Kurakurai:

 • Lokacin da Salim ya fara zuwa wajen mahaifin sa da bukatar a janye auren sa da Nafisa, abin daukar sauti ya fito wato “boom mic”.
 • Lokacin da abokan Salim suka zo gidan sa suna yabon kyawun matan da ya aura, ya kamata mamaki ya bayyana a fuskokin su a lokacin da Nafisa ta mike suka fuskanci cewa gurguwa ce.
 • Tun bayan auren Nafisa da Salim, ko sau daya me kallo bai ga wani daga cikin dangin ta ya ziyarce ta ba, duk da kasancewar sun san larurar dake damun ta gami da kuma rashin yardar Salim akan aura masa ita da aka yi, ya dace ko sau daya ne a ga mahaifiyar ta ko wani dan uwan ta ya ziyarce ta don sanin halin da take ciki a gidan auren ta.
 • An nuna wa me kallo cewa malamin da aka je nemawa Nafisa magani a wajen sa mazaunin jihar Gombe ne, (Kabiru Na Kwango) amma sai gashi titin da aka nuna kafin a nuna gidan malamin titi ne daya daga cikin na jihar Kano ba na Jihar Gombe ba, ya dace a nuna ainahin daya daga cikin titunan jihar Gombe ko don a tabbatar wa da mai kallo cewa an fita daga cikin jihar Kano ne an shiga jihar Gombe.
 • Har ila yau abin daukar sauti ya sake fitowa a lokacin da aka nuna Nafisa a cikin asibiti sa’in da taje duba Salim wanda aka yanke wa kafafuwan sa.
 • Lokacin da Salim ya roki gafarar Nafisa a cikin asibiti an ji karar kofa yayin da jaruman suka kalli kofar wanda a sannan ne Nafisa ta fadawa Salim cewa ga wanda zai aure ta nan. Yanayin fuskokin jaruman ya bayyana mamaki akan abinda suke kallo wanda ba’a nuna wa me kallo ba. Shin wanene wanda Nafisa zata aura din wanda ba’a bayyana fuskar sa ba? Ya dace a bayyanawa me kallo mutumin ko don tabbatar da gaskiyar abinda Nafisa ta fada gami da cire me kallo daga wasuwasi kan wanda Nafisa ta sake samu a matsayin masoyi, domin ba’a sani ba ko daya daga cikin masoyan da ta guje su a baya ne ko kuma wani ne na daban.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar gami da taba zuciyar me kallo, kuma labarin yayi nasara wajen rike me kallo har zuwa ga sakon da ake son a isar. Haka kuma fim din ya tabo wani bangare na abubuwan da suke faruwa a cikin al’umma domin an nuna butulcin da namiji gami da karshen butulu, sannan kuma an yi kokarin nuna darasi ga wasu ‘yan matan masu wulakanta saurayin da ba sa so wanda sau tari hakan yakan jefa su cikin matsala.

Wallahu a’alamu!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!