Connect with us

ADABI

Wakar ‘Nasiha Ga Mata’ Daga Faisal Da Indabo

Published

on

Matasan marubuta wakokin Hausa wato Adamu Yusuf Indabo kuma wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU da kuma marunuci mawaki Faisal Ahmad Bashir (FAB) su ne suka yi hadakar tunani da fasaha wajen samar da wannan waka ta ‘Nasiha Ga Mata’. Wakar da take wa mata nasiha musamman matan wannan zamani da a cikin su ne ake samun wasu wai masu fafutukar kwato ‘yancin mata, saboda ganin su fifita maza a kan mata da sanya rayuwarsu a karkashin mazan kamar rashin adala ne da kaskanci gare su.    Kuma suke kallon maza a matsayin abokan gabarsu maimakon abokan rayuwarsu. Wakar dai tana yin bayanin dukkan irin dama da ‘yanci da kuma gatan da Musulumci ya yi wa diya mace ne sabanin yadda wasu ke hure musu kunne, don son su dora su a keken bera. Ga dai cikakkiyar wakar kamar haka. Fatan a sha karatu lafiya:

Kunce musulunci ya barku zaman gida kunata ɗawainiya.

Haba kubar fadin haka Musulunci yai muku gata aduniya.

Ya baku mazaje dan sukula daku da ɗawainiya.

Ci da sha da tufatarwa dukka gaba daya.

Faisal rabu da wadancan yan hauragiya.

Su burinsu maza da mata su ta cudanya.

A ofis da tituna a bar da’ar Islamiyya.

A murkushe rayuwar aure a dau sharholiya.

Ka ji halin kawai da bin sharrin zuciya.

Mu dai ‘ya’yan aure ba za mu bi karya.

Hanyar kwarai kawai hanyar gaskiya.

Ba mu ce kar mace tai aiki ko cinikayya.

Tai kasuwanci aikatau don rifin asirin duniya.

Ta samu ‘yan sulalla don fita kunya.

Amma kar ta tozarta aure sunnar Himdaya.

Kuma ban da ta ta’addanci da fariya.

Ladanta na ga Allah Makagin duniya.

Musulunci yayi bayanin maza Asaman mata ba mai tankiya.

Ya ware hakkoki ga mazaje

Dan suyi da wainiya.

Ci da sha da tufafi dukka Gaba daya.

Akan mazaje nauyin dukka Yarataya.

Lafiya da gurin kwancin su Na duniya.

Dukka maza ke daukar nauyi Ko akwai mai tankiya.

Mace bana miji ko a wajan Bauta su gane gaskiya.

Mace bata limanci acikin jinsin Mazaje gaba daya.

Musulunci yai mana nuni Akan rauninsu nazuciya.

Murike su da kyawu suma Jinsun mune gaba daya.

Dan kafin zuwan Musulunci An ware su jinsiya.

Ba,a kulawa da su balle asasu a saggar duniya,

A kan haihu dan aji dadi Harma ai fariya.

Inna miji aka samu za ai murna harma ai tutiya.

Da zaran ance mace agareshi Bakin ciki ya sa mai aduniya.

Ajahiliya nake muku nuni Kafin zuwan Musulunci duniya.

An burne mata da yawa dan Gun wula kancin duniya.

Agaresu in suka barsu zasu Sasu da wainiya.

Sunyi gudun wula kanci da Talaucin duniya.

Musulunci yace mata rahama Ne agaremu gaba daya.

Mubar azabtar dasu murike su Karmubar su susha wuya.

Mubasu hakin su kar mu dan ne Suma sun zan ɗiya.

Akasa uku namiji biyu itama Abata kaso daya.

Kunji addini ba san rai Sai dai gaskiya.

A yau fadi suke musulunci Yai musu wariya.

Ya barsu zaman gida ko da Yaushe sunata da wainiya.

Kubar fadin haka Musulunci

Yai muku ko mai aduniya.

Yabaku mazaje dan su kula Daku da ɗawainiya.

Wai mace namiji wannan kalmar tasani dariya.

Ko afilin yaki ban ji mai sunan Kiba balle ki fariya.

Sheri na yahudu ne yasaka su Sukai kauciya.

Suka ce ko mai za muyi suma Mata Zasuyishi gaba daya.

Suka ɗauka duk dai dai mu ke Basa tunanin baya.

Wallahi mace ba na miji Nafada ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!