Connect with us

LABARAI

Zan Yi Iyakar Kokarina Wajen Cigaban Masarautar Malumfashi Da Katsina – Galadiman Katsina

Published

on

Tsohon mai sharia, Alkali Sadik Abdullahi Mahuta (OFR), Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi ya bayyana cewar zai yi iyakar kokarinsa a wajen kawo cigaban masarautarsa ta garin Malumfashi da jihar Katsina baki daya hakimin yayi wannan tsokaci ne a fadar sa dake garin Malumfashi a lokacin da yake zan tawa da jaridar leadership a yau mai fitowa kullum a gameda yun kurinsa na ciyar da masarautarsa ta garin Malumfashi gaba tareda kawo cigaban masarautar jihar Katsina bakidaya.

Basaraken ya cigaba da cewar wajibine a matsayinsa na amatsayin sa na daya daga cikin iyayen kasa kuma shugaban al-umma dole ne ya kasan ce mai adalci a wajan gudanar da jagorancin jama’a  a acikin adalci tareda kare mutuncin su da kuma kara bunkasa masarautar Malumfashi data Katsina baki daya sannan ya ummurci matasa da sauran al- umma gundumar kasar Malumfashi da Katsina bakidaya da suzama ja kadu na gari a wajan huddo dinsu na yau da kullum domin samun cigaba da kara samun zaman lafiya a kasar Malumfashi da Katsina da Nijeriya bakidaya

Tsoho mai shariar yakara da cewar yana mai matukar nuna farin cikinsa ga Allah suba hanahu wata ala da yabashi ikon kammala aikinsa na gudanar da har kokin sharia a Nijeriya lami lafiya lau kuma ya gama da jama’a lafiya sannan kuma Allah ya sake bashi wannan matsayi na galadiman Katsina hakimin Malumfashi afadar mai mai martaba sarkin Katsina dokta Alhaji Abdulmummuni kabir usman ya tabbatar masa da ita kuma sarkin Katsinan yana dashi a wannan mukamin in jishi yana godiya ga mai martaba tareda yan maja lisunshi da suka karramashi da wannan mukami yakara da cewar kuma zaiyi iya kokarinsa a wajan ganin masarautar Katsina ta kara samun daukaka tareda bunkasa a duk fadin jihar ta Katsina da kewayen ta bakidaya

Sannan kuma hakimin ya cigaba da kiraga al-ummar jihar ta Katsina tareda sauran jama’arsa na kasar Malumfashi da ke wayen ta da su cigaba da zaman lafiya da junan su a kowane lokaci domin Karin samun walwala da jindadi ga al-ummar jihar ta Katsina da kasar Malumfashi da ke wayenta bakidaya sannan ya sake ummurtar matasa da sucigaba da bin shuwagabani a koina suke tareda bin dokokin Nijeriya sauda kafa a matsayinsu na yara manyan gobe in jishi kuma shuwagabannin jibi in jishi da fatan Allah yacigaba da zaunar da kasar Malumfashi lafiya da jihar Katsina da Nijeriya bakidaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!