Connect with us

RAHOTANNI

Rikicin Masarautar Ibadan: Sabbin Sarakuna Sun Ki Halartar Taron Sulhu

Published

on

Akwai alamun baraka a tsakankanin sabbin Sarakunan da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya daukaka darajarsu, a inda mafiya yawansu suka sake kauracewa taron sasantawa da aka shirya a fadar  Popoyemoja, ta Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji, a jiya.

Taron wanda aka dage shi makwanni biyu da suka gabata, ya kara cin tura a jiya wanda ake ta kokarin yinsa domin kasha wutar da ta ta so a Masarautar.

Olubadan da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rashidi Ladoja, hankalinsu bai kwanta ba da hanyar da aka bi wajen daukaka darajar Sarakan, sa’ilin da Sarakuna kimanin Takwas daga cikin sabbin Sarakunan da aka karawa girman suka yaba wa gwamnatin a kan yanda ta baiwa Masarautar ta Ibadan darajarta.

Wadanda suka halarci zaman sulhun a jiya cikin zaman sirri sun hada da, Oba Lekan Balogun, Oba Amidu Ajibade da babban sarki Rashidi Ladoja.

Wadanda kuma suka ki halartar taron sun hada da, Oba Owolabi Olakulehin, Oba Eddy Oyewole, Oba Abiodun Kola-Daisi, Oba Lateef Gbadamosi Adebimpe da sauransu.

An ce, Oba Kola-Daisi, ya bayar da kwakkwaran dalili na rashin halartarsa wajen zaman sulhun.

Abin da ya sanya muka kauracewa zaman – Oba Olakulehin

Da yake Magana da manema labarai ta waya, Oba Olakulehin cewa yay i, sun ki halartar zaman ne sabili da wasu dalilai da suke da su.

Olakulehin,wanda ya yi maganar ce a madadin sauran, ya ja musu da cewa, akwai sauran gurabe guda hudu a jeron Balogun, wadanda ya kamata a cike su tun da jimawa, amma sun ki su cike su din.

Oba Olakulehin ya ce, ìBa mu je wajen ne ba saboda akwai batutuwan da ba a warware su ba. a jerin Balogun, akwai gurabe guda hudu da ya kamata a cike. Amma a maimakon a cike su sai suka nada wani sabon Iyalode, a fadar ba tare da tuntuba ba.

ìSun aiko mana da wasika cewa suna son cike wadannan guraben a jerin na Iyalode. Amma na Balogun fa? Wannan shi ya sanya ba mu je wajen zaman ba.

Sai dai sabbin Sarakunan suka ce zama na biyun da aka shirya bai yi daidai ba, domin bukukuwan Sallar Eid-el-Kabir.

Suka ce, duk wani sharadi da za a hada da shi a wajen taron sulhun sam kar ya shafi batun warware masu rawani da mukamai da aka ba su.

Ba a dai bayyana ainihin abin da sakamakon zaman ya kunsa ba ga jama’a ba, amma wata majiya ta shaidawa wakilinmu cewa an tsaya ne a kan yanda za a samar da dawwamammen zaman lafiya a Masarautar ta Ibadan.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: