Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Abubuwan Da Suka Kamata A Sani Dangane Da Mai Garkuwa Da Mutane Wadume

Published

on

Fitaccen wanda ake zargi gwani ne wajen iya garkuwa da mutane, kuma shugaban masu garkuwa da mutane, Bala Hamisu wanda aka fi sani da Wadume, wanda bayan cafkeshi a kan tafiya da shi ya jawo mutuwar jami’an ‘yan sanda guda uku da kuma wani farar hula guda daya wanda hakan ya zama babban abin takaici,  rana ta sake bacewa mai garkuwar yayin da sake fadawa tarkon  ‘yan sanda karo na biyu.

Jami’an ‘yan sandan  sun cafke madugun garkuwa da mtanen a Layin Mai Allo Hotoro da ke jihar Kano, a karkashin tawagar kwararru da suke aiki a karkashin shugaban ‘yan sandan Nijeriya (IRT) a ranar 20 ga watan Agustan nan da muke ciki.

Makonni da suka gabata, An yi zargin shi Hamisu Bala Wadume  ne ya janyo mummunar rashin jituwa a tsakanin jami’an tsaro na sojin Nijeriya da kuma ‘yan sandan Nijeriya.

Hankulan tawagar IRT ya karkata don kame Wadume ne tun a watan Maris na shekarar 2019 biyo bayan lokacin da suka amshi korafi daga wani mutum mai suna Sheriff Umar da ke karamar Kirikinua kudancin jihar Kaduna.

Mai korafin ya labarta musu cewar an yi garkuwa da dan uwansa mai suna Usman Mayo tun a ranar 15 ga watan Fabrairun 2019 a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba, sannan, masu garkuwan nasa sun bukaci kudin fansa na naira miliyan dari biyu N200m don su sake shi.

Bayanin ya kara da cewa, iyalan wanda aka yi garkuwa da shi din, sun cimma matsaya da wadanda suka sace dan uwan nasu kan cewar su biya naira miliyan tamanin da biyar N85 wanda suka biya a ranar 11 ga watan Maris na 2019 amma duk da haka wanda aka sacen ba a sake shi ba.

Ya ce, bayan da suka bayar da miliyan 85, sun kuma kara bayar da wani miliyan sha biyar N15m a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2019, wanda kudin fansar da suka biya ya kama naira miliyan 100 amma duk da hakan masu garkuwa da Usman sun ki sake shi, suna masu cewa dole ne fa sai iyalan Usman sun basu naira miliyan 200 kafin su sake shi.

A bisa wannan ne, tawagar jami’an ‘yan sanda masu aiki da kaifin basira, (Intelligence Response Team) a karkashin jagorancin ASP Felid Adolije suka tashi tsaye wajen gudanar da samame har suka cafke Wadume daga bisani suka gamu da farmakin sojoji wanda suka dauki Wadume zuwa bariki ‘Command Headkuarters’ da ke Jalingo.

A wannan harin, Insifekta Mark Ediale, Sajen Usman Danzumi, Sajen Dahiru Musa gami da wani farar hula guda daya sun gamu da ajalinsu biyo bayan illar da harsasan sojojin suka musu, a yayin da wasu kuma suka gamu da raunuka daban-daban.

Da aka kaddamar da bincike kan mutuwar ‘yan sanda ukun, an zargi Kaftin din sojan da ya umurci a sake Wadume sun yi musayar waya ta wayar tangaraho har sau 191 tare.

Hamisu Bala wanda aka haifesa a karamar hukumar Ibi ta jihar Taraba. Babansa dai sunansa Bala, shi Bahaushe ne, a yayin da mahaifiyarsa ta kasance ‘yar kabilar Tib daga karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai.

Sunan lakabinsa, ‘Mene ne ma ya sanya ake masa wannan lakabin’? domin yana yawan kuskure sai ake kiransa da ‘Wadume’. Shi Bahauce ne domin Kakansa ma ya kaura ne daga jihar Katsina. A lokacin da yake tasowa, shi Wadume yana sana’ar sai da kifi ne da kuma yin fenti tare da ‘yan uwansa.

Bala Wadume ya gawurta sosai gabanin zaben 2019, har ma ya fito neman takarar majalisar dokokin jihar Taraba mai neman wakiltar mazabar Ibi a karkashin jam’iyyar Young Democratic Party (YDP) sai dai ya sha kasa bai ci nasarar shiga majalisar ba.

A wani gajerun bidiyo da ya sake bayan jami’an ‘yan sanda suka kara cafke shi a karo na biyu, Bala Wadume ya shaida da kansa cewar, “Nine Hamisu Bala wanda yake da inkiya ‘Wadume’, ‘yan sanda suka zo Ibi suka kamani, da suka kamani, suna tafiya da ni sai soja suka bisu suka bude wuta har wasu ‘yan sanda suka rasa rayukansu.

“Daga nan suka daukoni suka kawoni Hedkwatarsu na soja suka yanke min sarkar da ke hanuna na gudu, tun daga na guda nake cikin boya sai yanzu ‘yan sanda suka sake kamani,” A bidiyon da aka sake a lokacin da ya sake fadawa tarkon ‘yan sandan Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: