Connect with us

SIYASA

Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ta Garkame Iyakarta Da Kwatono

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, ta garkame babbar iyakar ta da kasar Benin da ke Seme a jihar Legas. Kodayake ta sanar da hakan ne bagatatan a ranar larabar da ta gabata, inda wannan matakin na gwamnatin, ya janyo ritsawa da dubban mutane da ababen hawa da ke jigila kullum a tsakanin kasashen biyu.

Kamar yadda kafar Premium Times ta ruwaito, an karkame  iyakar ce a ranar Talata bayan an kama wasu manyan motoci shake  da kwayar ‘Tramol’ a Legas a cikin wannan watan.

Har ila yau, garkamewar  ta cigaba har zuwa safiyar ranar Laraba, inda hakan ya janyo  ‘yan kasar nan yin dandazo a bakin iyakar, inda suka shiga cikin tunanin ko kilan, za a daga masu kafa su samu shigowa cikin Nijeriya.

Bugu da kari, rufe iyakar ya ritsa da wasu yan kasuwar kasar Benin da ke son koma wa gida bayan da suka shigo cikin kasar nan gudanar da hadar-hadar kasuwancinsu a wasu kasuwannin da ke cikin jihar Legas.

Wasu bayanai sun ce, garkame  iyakar ba tare da wata sanarwa ba ya shafa suna kumfar baki a dandalin sada zumunta ranar Laraba.

Kakakin rundunar hukurmar kula da shige da fice ta kasa Mista Sunday James kafar Premium Times ta tura masa sakon karta kwana a kan batuun, sai dai bai bai maido da amsa ba.

Sai dai, hukumar Kwastam sanar a cewa, an garkame   iyakar ce sakamakon  wasu dalilan tsaro.

A cewar kakakin  hulumar ta Kwastam Joseph Attah an garkame iyakar ce saboda ana  gudanar da wani aiki na hadin gwuiwa da jami’an tsaron da ke aiki a iyakar Seme.

Joseph Attah  ya kara da cewa, za’a kai kwamaki kafin a kammala wannan aiki, kuma mu na iyakar bakin kokarin mu domin ganin aikin bai shafi matafiya ba.

Kakakin ya yi kasa a gwiwa wajen gaza yin karin haske a kan ko an fitar da wata sanarwa kafin fara aikin da ya jawo aka rufe iyakar wanda yin hakan kan iya gurgunta harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika ta yamma.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!