Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Sabon Galadiman Katsina Ya Yi Hawan Daushe A Malumfashi

Published

on

Tsohon mai shari’a Hon. Sadik Abdullahi Mahuta, OFR, kuma Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi da ke jihar Katsina ya gudanar da taron Hawan Haushe da dashen itatuwa tare da bayar da tallafi ga mata masu ’ya’ya marayu, wadanda mazajensu suka rigamu gidan gaskiya da zawarawa wadanda su ma mazajensu su ka rigamu jidan gaskiya da sallamar ’yan bursina goma sha daya masu kananun laifuka da ke tsare a gidan yarin Malumfashi da dai sauran makamantansu.
Taron walimar wanda ya gudana a makarantar sakandiren gwamnatin jihar Katsina da ke unguwar danrimi a Malumfashi a ranar Asabar da ta gabata kuma taron walimar ya samu halartar dimbun al’umma da su ka fito daga sassa daban-daban na jihohin Najeriya kuma ya kunshi magaddai masu unguwanni na garin Malumfashi da sauran hakimai na wadansu kananun hukumomin jihar Katsina da malamai wadanda suka gudanar da wa’azuzzuka ga al’umma da maroka makada da mawaka da dai sauran makamantansu.
Manyan baki a wajen wannan taro sun hada da gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, da Sarkin Katsina Dakta Abdulmumini Kabir Usman wanda ya samu wakilcin kauran Katsina hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir Rimi da dai sauran makamantansu.
A jawabinsa ga al’ummar jihar Katsina uban taron kuma Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya umurci al-umar jihar ta Katsina dasu cigaba da zaunawa lafiya da junansu sannan kuma ya nuna farin cikin sa ga sabon galadiman Katsina Hon: jostis Sadik Abdullahi Mahuta OFR da sauran “yan kwamitin da suka shirya wannan taro mai mahimmanci ga al-ummar jihar Katsina dasu bada
Tasu gudummawar a wajen tabbatar da ingancin ilimi tundaga firamare zuwa sama.
Anasa jawabin a matsayin na uban kasa kuma sarkin Katsina Dakta Abdulmumini Kabir Usman wanda yasamu wakilcin kauran Katsina hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir Rimi bayan ya nuna farin cikin sa ga wadan da suka shirya wannan taron mai matukar muhimmanci ga al-ummar jihar Katsina sannan yayi kira ga sauran hakimai na jihar Katsina da su cigaba da shirya irin wannan taron domin Karin hadin kan jama’arsu da daukaka masarautarsu da masarautar Katsina baki daya.
A cigaba da nasa jawabin kantoman riko na karamar hukumar Malumfashi HON. Alhaji Aminu Waziri Malumfashi ya taya mai martaba galadiman na Katsina hakimin Malumfashi murnar gudanar da wannan taro a wannan lardi na Malumfashi domin karin samu hadin kan al-ummar masarautarsu da sauran al-umma baki daya sannan ya ummurci al-ummar ta Malumfashi dasu cigaba da girmama shuwagabanni injishi mussamman gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin gwamnan jihar ta Katsina Alh. Aminu Bello Masari Dallatun Katsina domin cigaba da samun ayyuka na cigaban karamar hukumar Malumfashi da jihar Katsina tare da goyama masarautar galadiman na Katsina hakimin Malumfashi baya domin Karin samun zaman lafiya da bunkasar masarautarta Malumfashi data Katsina baki daya.
A karshen nasa jawabin mai gaiya mai aiki tsohon mai shari’a Hon. Jostis Sadik Abdullahi Mahuta OFR galadiman Katsina hakimin na Malumfashi bayan ya kammala yima gwamnan jihar Katsina barka da zuwa Alh. Aminu Bello Masari da kauran Katsina hakimin rimi Alh. Nuhu Abdulkadir Rimi da sauran hakimai da suka samu zuwa wannan taro da dumbin jama’a da suka fito daga sassa daban-daban domin taya shi murnar gudanar da wannan taro injishi yana yima kowa fatan alkhairi na komawa gidansa lafiya sannan ya tabbatar ma jama’a zai cigaba dayin jagoranci a cikin adalci a masarautar Malumfashi cikin jihar Katsina baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!