Connect with us

Da dimi-diminsa

Kujerar Majalisar Tarayyar Ta Katagum: Kotu Ta Umurci INEC Ta Kwace Satifiket Din Da Ta Ba Umar Sarki

Published

on

Nasarar da ta baiwa Abdulkadir Umar Sarki zarafin zama dan majalisar tarayya da ke wakitar mazabar Katagum a majalisar wakilai ta kasa na sama na dabo, inda kotu ta umurci INEC ta sake zabe a rumfunan zabe guda bakwai bisa gano tafka aringizon kuri’u.

A zaman yanke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisun tarayya a Bauchi ta yi a yau Alhamis karkashin jagorancin Alkali Justice Bello M. Tukar ya ayyana zaben a matsayin inkonkulusuf, yana mai shaida za a sake zabe a rumfuna guda bakwai.

Kotun ta umurci a gudanar da sake zaben cikin kwanaki sha tara da yanke hukuncin.

Wannan hukuncin ya biyo bayan karar mai lamba EPT/NASE/BA/4/2019, wanda Ibrahim Mohammed Baba na jam’iyyar APC ya kai, inda yake kalubalantar nasarar Abdulkadir Umar Sarki na jam’iyyar PRP da wasu hudu.

Kotun dai ta soke zaben mazabu bakwai da umurtar a sake ne a bisa ganowar da ta yi na cewar wadanda suka kada kuri’u a mazabun sun zarce mutanen da suka yi rijista wanda hakan ya bai ma wanda ya ci na farko nasara.

Wakilinmu ya labarto cewar kotun ta umurci INEC ta soke takardar shaidar da ta bayar tun a farko a ranar 23 ga watan 2.

A wani sabuwa kuma Wakilinmu ya labarto cewar kotun ta kuma yanke hukunci a tsakanin Halliru Dauda Jika (APC) da Sanata Hamma Misau (PDP), inda kotun ta kori karar da cewar karar bai da inganci.

Hamma Misau dai ya kai koke yana kalubantar nasarar Jika a zaben da aka gudanar kan kujerar sanatan Bauchi ta tsakiya a majisar dattawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!