Connect with us

Uncategorized

Jama’ar Rafi Na Goyon Bayan Dawowar Bojoh Karo Na Biyu

Published

on

Matasa a karamar hukumar Rafi sun jaddada goyon bayansu na sake tsayawar Honarabul Garba Tanko Bojoh, tsohon shugaban ALGON na kasa sake dawo wa karo na biyu a matsayin shugaban karamar hukumar, matasan sun bayyana hakan a Kagara lokacin da suka ziyarci tsohon shugaban don nuna goyon bayansu gare shi, a kakar zaben kananan hukumomin jihar Neja mai zuwa cikin watan Nuwambar wannan shekarar da muke ciki.

Da yake zantawa da manema labarai a Kagara juma’ar makon nan, Malam Jamilu Isyaku. Ya ce Honarabul Bojoh ya shugabanci karamar hukumar nan tsawon shekara uku kuma shaida ne a kan irin gudummawar da ya samar na ci gaba, domin karamar hukumar Rafi muna daga cikin kananan hukumomin da ke da matsalolin rashin ruwan sha mai tsafta, amma kusan dukkanin mazabummu har da na cikin karkaru ba inda Bojoh bai gina famfon burtsetse ba, haka duk da matsalolin tattalin arzikin kasa da aka fuskanta a farkon mulkin APC, duk karkarun da ke matsalolin hanya musamman a lokacin damina, Honarabul Bojoh ya tabbatar karamar hukumar Rafi ta taka rawar gani, wadannan dalilan kadan ne daga cikin dalilan da suka sa mu matasa da dattawa, musamman mata da ke cikin karkaru da na cikin gari bai wa Honorabul goyon bayan tsayawa takarar wannan kujerar ta shugabancin karamar hukumarmu.

Amsa kiranmu na sake neman wannan matsayin tamkar ruwan sanyi ne tsohon shugaban ya sanya mana a zukatanmu, don haka za mu jajirce ruwa da iska, safiya da maraice don neman amincewar jama’armu wajen sake dawo da shi a kan wannan kujerar karo na biyu. Mun sani karamar hukumar Rafi na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fuskantar masu garkuwa da jama’a wanda har yanzu akwai daruruwan jama’a da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira wadanda aka koro daga cikin karkarun. Mun ga kokarin da ya yi a zangonsa na farko wajen dakile ci gaba da wannan barazanar, mun shirya ba da lokacinmu ta hanyar kuri’a muddin jam’iyyar APC ta amince da kudurinmu waje sake ba shi wannan damar,  mu kuma za mu tabbatar jam’iyyar APC ba ta ji kunya ba, domin ya rika mun ga abin da ya yi wa karamar hukumarmu.

Jama’a dai da dama a karamar hukumar ta Rafi sun bayyana cewar a shirye su wajen bai wa APC hadin kai ta hanyar ba ta kuri’unsu muddin suka amince da bai wa tsohon shugaban karamar hukumar damar sake jagorantar karamar hukumar a karo na biyu, domin ya yi sun gani kuma sun ga irin rawar da ya taka a shekaru hudun da suka gabata.

Zuwa yanzu dai tsohon shugaban karamar hukumar ta Rafi, Honarabul  Garba Tanko Bojoh zai fuskanci tankiya ne da sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, Alhaji Modibbo Muhammad wanda shi ma ya nuna aniyarsa na yin takarar a inuwar jam’iyyar ta APC a zaben kananan hukumomin da za a gabatar a karshen watan Nuwamban nan bayan jam’iyyun siyasa sun kammala zaben fid da gwani.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: