Connect with us

RAHOTANNI

Ka Yi Addu’a Kawai Wajen Neman Aure Da Kuma Zamantakewar Auren

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Asabar. hakika na yi farin ciki da kirkiran wannan shafi na musamman domin masoya tare da isar da sakon da muke son isarwa ga ‘yan’uwa masu gudanar da soyayya. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya. Ni dai zan dan yi tsokaci ne a kan neman aure da kuma zamantakewar auren.

Aure wata jami’a ce, kamar yadda muka sani a baya, mai rassa daban-daban, kowani reshe da abin da yake koyarwa, ka ga matannan da za ka auro, ka roki Allah kawai ya ba ka ikon mallakarta gaba daya, amma ba wayonka ko iya zabinka ba. Na ga wani dattijo da ya auro wata matashiya, kullum wani fegi na bala’i ake budewa a cikin gidansa, har sai da zaman gidan ya gagare shi, banda bakaken maganganu da muguwar fata gami da raina masa hankali da arziki a gaban sauran ‘ya’yansa ba abin take yi. Abin da ban sani ba muguwar kauna ce ta makure shi ko tsabagen hakuri ne, Allah ne masani, ba abin da yake yi sai dai ya fito kofar gida ya kama kofar ya yi jungum kamar wanda aka yi masa mutuwa.

Na ga wadanda suna cikin zaman-zamansu da iyalinsu allurar kara aure ta soke su, suka ta shi suka yo amare, wallahi sai da suka sayar da kaddarorinsu ciki har da gidajensu suka kama haya da kudin, duk dai a dalilin matansu. Akwai wacce ta sa aka kori mijin a wajen aiki, kuma ba ta da niyyar rabuwa da shi, wata kuwa raba shi da ‘yan’uwansa ta yi gaba daya, don yana da dan abin hannunsa, ta damka masa nata ya rike su hannu bibbiyu, kullum sai ya yi musu goma na arziki, a karshe ta kwaso ‘yan’uwanta da danginta suka tare a gidansa, ba wani dan’uwansa da ya isa ya tafi gidan, ta yanke duk wata alaka a tsakaninsu.

Wata kuwa ba ta shiga gidan ba sai da ta saka shi ya rabu da uwar ‘ya’yansa, ta raba shi da abokansa, a karshe ta dauke shi daga gaban uwayensa ta yi kudu da shi, sai yadda ta so za a yi, wai kuma shi ne maigidan, abin takaicin a duk wadannan jarabawoyin da nake gaya muku ba kwadayi ya kai mazajen ba, wallahi kaddara ce kawai, don sun fi matan nasu komai da ka sani amma sai yadda matan suka yi da su, ka ga kenan akwai bukatar rokon Allah ya ba ka mata ta gari kawai.

Na ga wata da take yi wa mijin duk ladabin da yake bukata, kuma sam ba za ka ga wani nata a gidan ba bare ka ce kaza da kaza, ana yaba mata rashin kwadayi da kamun kai, sai dai ba nan gizo yake sakarsa ba, yaran nata kab dinsu ba mai dabi’u na kwarai, tun suna kanana ba wanda ya isa ya tabe su ko ya ce zai aike su, a takaice dai ba tsayayyiyar uwa ba ce, yarannan kowa da dabi’unsa, sam ba su biyo halin uban ba, duk da haka lalacewar na gaban bai sa ta yi la’asar ta gane inda ake fuskanta ba, ba a je ko’ina ba uban yaran yana ji yana gani sun fi karfinsa.

Wata kuwa tausayi ne ba ta da shi, zai yi wahala ka ga ta adana wani abin da maigidan zai shigo da shi, ba kwashewa take yi ta kai wani wuri ba, amma sam ba ta damu ne da tattali da adani ba, komai ya shigo da shi sai an lalata, ba za ta tsawata ba, in wani abinci ya kawo wanda in aka ririta shi zai iya kai su wata guda suna gurzarsa, to a kwana uku za su gama da shi, in ya ba da shawarar a gwada yin amfani da wani abu sai ta ce matsayinsu ya wucenan, kuma ba za a yi din ba bare ya samu ya huta.

Akwai ballagaza, tana da mijinta na aure wanda ya aure ta tana budurwa, amma ‘ya’yanta hudu kowa ubansa daban, abin da zai ba ka mamaki mijin nata yana sane da duk abin da take yi, amma bai rabu da ita ba, a lokacin da nake magana da makwabtansa na ce “Amma fa duk da haka in ya san cewa yarannan ba nasa ba ne zai iya koranta a gidan” suka ce “Wallahi yana sane da haka” na ce “Kamar ya?” Suka ce ai an sha tabka rikici a kan haka, kuma shi din ya san uban kowa in ba wanda Inyamuri ya yi cikinsa ba” kai hatta hanyar da kwartayen suke shiga gidan ya sani, amma yana zaune da matar, na ce zuciyarsa ta mutu.

Wata kuwa tana da halayenta na kwarai sai dai ba ta zaman gida, ba zinace-zinace take yi ba, amma ba za ta taba zama a dakinta ba, kullum cikin nemo masa rigima, yana fita za ta sa kafa ita ma ta shiga makwabta, bai da aiki sai yi mata kashedi, amma bai iya tsinana komai ba, in ‘yan’uwansa sun janyo hankakinsa ya yi kamar zai dauki mataki, yana komawa gida suka yi ido hudu da shi ba ka sake jin wani abu, tamkar an aiki bawa garinsu.

To idan ka fi mace komai ciki har da shekaru da kudi da ilimi gami da wayewa amma sai abin da ta yi, ya kake gani in ta dara ka komai? Shi ya sa muke cewa in kana da kyau ka kara da wanka kawai, sau nawa muke ganin malamai suna wa’azi a waje matansu suna kware musu sutura, in zama ka yi wurin matasa nan za ka ji wasu suna fadin ma-sha’an da suke yi da matan masu kudi ko milki, hatta maganganun shaye-shayennan wallahi ba a bar su a baya ba, wata fitinarma bana mafiyawancin ‘yan mata sun ajiye hijabi sun dauko gyalulluka, na fadi wannan maganar wani ya ce wallahi har da matan aure, don haka bari na komo kanki kawai.

Ya kamara idan namiji ya tashe neman aure, to ya zama mai mika lamarinsa ga Allah, ma’ana ya dage da yin addu’a kawai, domin ita ce mafita ga zamantakewar auren wannan zamani.

Sakon Daga Mammam Barista, Kaduna.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: