Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk ( 58)

Published

on

An Keta Mulkin Aswadu Dan Sauda’u Can wajen Sulusun dare Hamdiyatul’aini ta tashi ta yi alwala ta yi nafilfili kamar yadda ta saba, da lokacin Sallah ya yi ta umarci daya daga cikin jama’arta da ya yi kiran Sallah, sannan tana daga wurin da ta yi bacci ta bisu Sallah.

Lokacin da gamzaki ya keto an fara samun faifayewar gari madaukaki, sai ga jerin gwanon wasu tsuntsaye a sama wadanda dan-Adam ba iya tantance adadinsu ba, suna shawagi kai ka ce suna rera waka ne, a karo na farko sun wuce, daga baya kuma sai ga wasu tsuntsayen dangoginsu su ma sun zo sun wuce masu launin kore su ma ba a iya kiyaye wa da adadinsu. Daya daga cikin masu lura da garin ya ce, Allah da iko yake, dubi wani bakon al’amari da ba mu taba ganinsa ba.

Bayan shudewarsu da misalin rabin sa’a, sai suka ji rurin amalen rakumin nan gami da wani irin feshin wuta, an yi haka kamar marra uku sai kuma suka daina jin komai.

Sarauniya Hamdiyatul’aini ta dube shi ta ce, “ Shin haka wannan alkarya ke fama da al’amura na sihirce-sihirce .”  Ya ce, “ Ranki ya dade mu kan ji wasu abubuwa kamar haka, amma ba mu taba jin ko ganin abin da yake faruwa a yanzu ba, wannan fa wani al’amari ne dake alamta wani bakon abu da yake faruwa ko yake shirin faruwa.”

Sai daya daga cikinsu ya ce da babbansu a yi min uzuri zan dan kewaya, bayan tafiyarsa da ‘yan dakikoki sai ya dawo ya durkusa gabanta ya yi gaisuwa irinta sarakai. Babbansu ya ce, “ Ka ga sakarai, yanzu mecece fa’idar haka, ai mun san ‘yar sarki ce tun da fari, ta yaya kuma za ka yi mata gaisuwar sarakai, yalla ko dai dama ka san da wani lamari a boye?”

“ Bincike na gabatar a halin yanzu, na samun yakinin ita ce baiwar Allah din nan da na baku labarin za ta zo ta fitar da mu daga kangin da muke ciki.” babbansu ya dube ta ya ce, “ Ranki ya dade me yasa kika boye mana girmanki da al’amarinki, mun jima muna sauraron wannan lokacin, yau ita ce ranar da za mu samu ‘yancin yin ibada kamar ko wace alkarya.”

Ta ce, tun da kun fahimci haka ai sai mu yi haramar shiga gari don fuskantar abin da ke gabanmu. “ Maza ku yi niyya mu isa gare shi.” Suka jawo dawakinsu suka haye, ta tsaya aka yi addu’a sannan aka ci gaba da tafiya.

Da isarsu kofar fada suka samu ya fito cikin irin shigar da ya saba, “ Ranki ya dade wancan shi ne sarkinmu.” Hamdiyatul’aini ta ce, to ai an gaya min bisa kilagon giwa yake yakinsa, ya aka yi yau na ganshi kan doki?” in ji ta. “ To wala’alla dai ko alkadarinsa ne ya karye ko kuma an gaya masa ne kada ya fita a waccan shigar.” Sai ta ce  “ Babu shakka wannan mutum Allah ba shi girma, masha Allah ga muni, amma fa girmansa da karfinsa da muninsa da duk abin da yake takama da shi bai na gawurtaccen da na hallaka a baya can fadar da nake koyon al’amuran yaki ba,” zancen zuci kenan.

Ta mayar da kamanninta na wancan lokacin kamar cewa ita namiji ce, ta ce ku dan dakace ni zan je na tattauna da shi. Ta tunkare shi kai tsaye ba tare da wata fargaba ba, saboda dabarar yaki sai ta rage kamar taku hamsin tazara tsakaninta da shi ta tsaya, ta fara yi masa magana kamar cewa ita kurma ce domin kada ya ji muryarta ya gane ta saboda ta san Jassasa ta ba shi labarin zuwanta.

“ Yau ga wani bakon al’amari, kai mahayi idan kana da magana ka zo kusa dani bana kisa sai ga wanda ya amsa sunansa gwarzo, dokina kadai idan ya bangaje ku kai da dokinka sai dai wasu ba dai ku ba, bana fidda makami sai ga wanda sunansa ya yi nisa a duniyar mayaka, ga ka yaro baka kai matsayin matashi ba, kai da dokin naka nawa kuke,? Fadi abin da kake bukata na biya maka ko kuma na bautar da kai cikin bayin da ba bayi ba.”

Hamdiyatu’aini ta sake matsawa kusa da shi, ya rage saura misalin taku ishirin, sai ta sakko daga bisa dokinta, ta sake ganin ta kankance a kansa. Yana tsaye tana zagaya shi, shi kuwa ya dauki abin kamar wata almara, ba ya waigawa sai in ta zo ta gaban dokinsa sai ya kalle ta ya yi dariya.

An yi zagaye na biyu, cikin zagaye na uku ta zo daidai kafuwan dokinsa na baya, da zare takobin da sare kafafuwan dokin duka bai sani ba kawai sai jinsa yayi a kasa teem, dokin ya yi wata irin kara, Aswadu ya yunkura zai mike tsaye ya ga babu hali dokinsa ya danne shi, ga kuma doki babu kafafuwan tashi.

Ya yi ta yunkurin tashi, amma ina babu halin hakan, ya fusata ya zare takobi, ta sare hannun da yake rike da takobin, takobin yafadi can gefe guda, amma saboda jarumtaka ya sanya daya hannun zai jawo takobin amma ina! Ta yi nisa da shi. Daga baya kuma sai ta jiyo gunjin rakumin nan a bayan wata zahzah, ta yi tattaki izuwa wurinsa, ta dube shi ta ce, ba an ce kana aman wuta ba, to yanzu ka yi aman wutar, ga ubangijin can kwance cikin jini fito ka kai masa agaji.” Ya sake yin wata irin gaza, ina sai dai hayaki kawai hayakin ma ba mai zafi ba.

Ta dawo ga Aswadu ta dube shi ta ce, au har yanzu baka samu ikon tashi ba, yanzu ne sa’adda za ka yi yekuwa a kawo maka dauki daga sashin aljanu ko abin da ya yi munasaba da hakan. Tana gama fadar haka a wannan sa ‘a sauran jama’arta sun zo amma sun kasa karasowa saboda kwarjininsa, ta sanya hannu ta janye rawanin da ta shamukance fuskata, “ Ni ce Hamdiyatul’aini ‘yar manoma mai takama da asalin talakawa masu neman na kansu, sai ta daga murya tana mai shelanta cewa “ Ya ku taron aljanu babu wani daga jinsin aljanu ko shaidanu ko ifritai da zai iya kawo wa Aswadu dauki yau ga zakin da namun dawa ke tsoron afka masa a kwance karkashin ikon wata baiwar Allah mace ba namiji ba.”

Da Aswadu ya duba ya ga ashe ma mace ce a kansa, da ya yi wata irin kururuwa ya kama dammarar dokin nasa sai ta ga ya raba shi da kasa ya jefe ta da shi, da ta sunkuya dokin ya wuce ya yi karo da wata bishiya kai ka ce wata iska ce aka yi mai karfi ta tumbuke bishiyar nan, wata kura ta yi sama kamar ana guguwa. Ya yunkura zai tashi ina babu hali kafafuwa sun karairaye, kawai sai ta ga hawaye yana fitowa daga idanunsa.

Wani daga cikin su ya karaso ya ce “ Kai! Yau ga Aswadu yana kuka, ta ce, ina mai yi maku rantsuwa da Allah ba kukan wuya ba ne kuka ne na bakin cikin abin da bai yi tsammani a rayuwarsa ba, ta dube shi  sosai ta ce, wohoho! Ka sani mu musulmi ne da muka yi imani da bautar mahalicci sarki daya da ba shi da kini, babu wani da abu Allah ya halitta ko wani dan-Adam ya kirkira da zai dawwama a doron kasa sai ya kare, illa zatin Allah kadai shi zai wanzu, “ Wannan Sunnar Allah ce, kuma ba zaka taba samun sauyi a wannan sunnah ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: