Connect with us

KANNYWOOD

Waka Ta Yi Min Abubuwan Da Ban Yi Zato Ba – Aminu Genius

Published

on

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da MAWAKI AMINU GENIUS, Wanda A Ka Fi Sani Da (Son of Jigawa).

Da Farko Za Mu So Mu Ji Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka.

Jama’a Assalamu Alaikum ni dai sunana Aminu Haruna, wanda a ka fi sani da Mr. Genius A.K.A Son Of Jigawa. Ni haifaffen Karamar Hukumar Kiyawa ne da ke jihar jigawa. Na yi karatuna na Firamare a Zariya, na yi Sakandire a Command Secondry School da Ahamadiya. Sannan na yi karatuna na Degree wato B.sc a Bayero Unibersity, Kano, inda na yi karatu a sashin koyar da aikin jarida wato Mass Communication, kuma yanzu haka ina karatuna na Masters a Communication Studies a nan dai Bayero Unibersity din.

Ya Ya A Ka Yi Ka Samu Kanka A Cikin Harkar Waka?

Eh to gaskiya, Waka abu ne da nake so tun ina Sakandire, saboda makarantar da na yi (boarding school) ce, to akwai wani abokina Don AbdulAziz muna zama da shi yana min kida da hannu ni kuma ina rera Waka. To haka dai mu ka fara da wasa da wasa, har kuma zuwa yanzu. To a takaice dai tun da dadewa ni Waka ta na jinina ne, ina son Waka sosai.

Duba Da Cewa Ita Waka Ta Na Da Bangarori Ne Da Kuma Salo Daban-Daban Kai Wane Bangare Na Waka Ka Dauka?

Gaskiya ni ina yin wakoki ne na (Rap) wato ina yi ne da salo na (Rapping). Da farko a (Rapping) din ma ina yin irin wakokin soyayya ne kawai, to amma yanzu ina yin Waka ne a kan wani abu da ya ke damun al’ummarmu ko a kan wani abu da ya shafe su kai tsaye. Saboda haka wannan shi ne irin salon da na ke yin wakokina a kai.

Duk Da Cewa Ka Ce Ka Dade Ka Na Sha’awar Harkar Waka, Amma A Lokacin Da Ka Yi Yunkurin Shiga Harkar Wakar Gadan-Gadan, Wane Irin Kalubale Ka Samu?

Eh to kasan a wannan yankin namu na Arewacin kasar nan, Waka ba abu bace da ka na zuwa ka ce za ka fara za a ba ka goyon baya ba, a gaskiyar magana na samu kalubale da yawa tun daga cikin gida har zuwa waje. Saboda gaskiya ban samu goyon bayan iyayena ba a kan yin Waka har sai da na gama Degree na farko a Jami’a. To a nan ne su ka ce to tunda na gama makaranta lafiya sun san waka ba za ta hana ni komai ba yanzu, to shike nan tunda ina da sha’awar harkar wakar to in je Allah ya taimaka.

Mawaka Da Yawa Za Ka Ga Su Na Da Wasu Mawaka Da Su Ke Koyi Da Su A Cikin Wakokinsu, Kai Ma Ka Na Da Wani Mawaki Da Ka Ke Kallo A Matsayin Tauraro Wanda Ka Ke Koyin Irin Salon Wakokinsa?

Kasan Waka ita aba ce da a ke so ta ringa zuwa da wani abu na daban. Babu yadda za a yi ka na mawaki a ce babu wani mawaki da ka ke jin dadin wakokinsa, amma jin dadin wakokin mutum ba ya na nuna ka na kwaikwayonsa ba ne. Domin kuwa su ma wadanda su ke burge ka din wani salo ne nasu su ka zo da shi har su ke burge ka ba wai wasu su ke kwaikwaya ba, to kaima in dai ka na so ka burge wasu kai ma sai ka yi da naka salon ba wai ka ringa kwaikwayon wasu ba. To gaskiya ni ba na kwaikwayon wani mawaki a cikin wakokina. Kamar yadda na fada maka ina jin wakokin mawaka sosai, amma ko kadan ba na kwaikwayon wakar kowa. Ina da burun inga ina waka kamar wane, amma ba ni da burin kwaikwayon wakar wane, wannan shi ne gaskiyar magana. Ni ka ga yanzu ina wakoki ne na (rap), amma zai wahala ka same ni ina jin wakokin (rap), na fi jin wakokin da ba na (rap) ba musamman wakokin mawaka mata.

Yanzu Ka Samu Kamar Shekara Nawa Da Fara Yin Waka?

Kamar yadda na fada maka a baya na jima ina son harkar waka, amma da fara rubuta waka tawa ta kaina na fara ne wajen 2015 ne.

Daga Lokacin Da Ka Fara Waka Zuwa Yanzu, Wakokinka Sun Kai Kamar Guda Nawa?

To zan iya ce maka wakokina kala biyu ne, akwai wadanda na yi da kai na ni kadai, akwai kuma wadanda mu ka yi da mutane daban-daban a kuma lokuta daban-daban. Idan wakokin da na yi har wanda na yi da mutane ne to sun fi guda dari gaskiya, amma wakokina nawa na kaina wanda na yi ba su wuce guda sha biyar ba.

Izuwa Yanzu Ka Taba Fitar Da Kundin Wakokinka Kuwa?

Eh a shekarar da ta wuce wato 2018 na saki wani kundin wakokina wato (Album) mai suna “Son Of Jigawa” inda na fito na nunawa mutane cewa ni fa daga Jihar Jigawa na fito kuma ina alfahari da ita. To daga wannan lokacin ne na samu wannan sunan na “Son Of Jigawa” domin yanzu gaskiya an fi sani na ma da wannan sunan fiye da sunan da na fito da shi wato Genius.

Idan Na Fahimce Ka Wannan Kundin Na Son Of Jigawa Shi Ne Kundin Wakokinka Na Farko Kenan?

Eh Son Of Jigawa shi ne kundin wakokina na farko izuwa yanzu.

Duba Da Cewa A Nan Arewacin Najeriya, Kannywood Ita Kadai Ce Masana’anta Guda Daya Da Ta Ke Tafiya Da MaWaka, Kuma Ga Shi Ku Wakokinku Ba Irin Wanda A Ke Amfani Da Su Ba Ne A Cikin Masana’antar, Shin Ka Na Ganin Wani Lokaci Za Ka Iya Ajje Salonka Na Wakokin Hip-Hop Domin Kai Ma Ka Samu Damar Da Za A Ringa Damawa Da Kai A Cikin Masana’antar?

To shi daukaka ta a ji ka ko a san ka lokaci ne, duk wanda ka ga ya haska duniya ta san shi to lokacinsa ne ya zo. Saboda haka ba zan iya barin salon (hip-hop da Rap) da na ke Waka da shi ba, kawai don ina so a ringa saka wakokina a fina-finai ba. Domin da wannan salon ne na ke samun cikakkiyar damar isar da sakon da ya ke cikin zuciyata. Kuma ni ina mamakin wadanda za ka ga su na warewa cewa su iya maWakan nanaye ne ko na hip-hop kawai, ni a ‘yan kwanakin nan ma na yi wakoki sosai da maWakan nanayen, su na dora baitikansu ni kuma ina dora (Rap) dina.

Idan Ka Na Tattaunawa Da MaWaka Za Ka Ji Wasu Su Na Fada Maka Su Sun Dauki Waka Ne A Matsayin Sana’a, Wasu Kuma Sai Ka Ji Sun Ce Su Sun Dauki Waka Ne Amatsayin Nishadi, Kai Me Ne Ne Matsayin Waka A Gurunka?

Ni na dauki Waka ne a matsayin sana’ata, domin da don nishadi kawai na dauki Waka ai da ban fito na nunuwa duniya cewa ni mawaki ba ne ba, da sai kawai in ta nishadina ba tare da wani ma yasan ina yi ba. Ita Waka dukanta nishadi ce tabbas, amma ta hanyar nishadin kuma a ke samun wani abu, ka ga a she ta zama sana’ar kenan. To ni dai gaskiya a gurina Waka sana’a ce ba wai nisahadi kawai ba.

Kamar Ku MaWakan Hip-Hop Ta Wacce Hanya Ne Ku Ke Samun Kudin Shiga Daga Wakokinku?

Eh to mu dai maWakan hip-hop gaskiya mun fi samun kudi ta hanyar zuwa taruka wato (Shows), ko kuma idan ka yi kundin wakoki wato (Album) shi ma za ka saida CD ka samu kudi. Sannan wasu suna dorawa a Youtube akwai matsayin da idan ka kai za su fara biyanka. MaWakan hip-hop gaskiya muna samun kudi ne ta hanyar (shows) ko kuma sai da kundin wakoki.

Ya Za Ka Iya Bayyana Alakarka Da Sauran MaWakan Hip-Hop Da Kuma Sauran MaWaka Duba Da Cewa Kai Ma Ka Samu Shekaru Masu Yawa A Cikin Wannan Harka?

To Alhamdulillah ni gaskiya ina da kyakkyawar alaka da kowanne mawaki, ba ni da wani mawaki guda daya da zan ce maka ina da wata matsala tsakanina da shi a maWakanmu na hiphop a Arewacin Najeriya gaba daya. Idan ka duba tun daga kan manyan irin su Bily O, irin su Dr. Pure da sauran manyan maWaka dai da lokaci ba zai bari in ambato su duka ba. Kuma duka a na zaman mutunci da girmama juna. To gaskiya ni ina mutunta kowa kuma ni ma a na mutunta ni, hakika ina jin dadin yadda abu uwan su ke tafiya.

To Izuwa Yanzu Ku Na Da Wata Kungiya Ne Guda Daya Wadda Duka MaWakan Hip-Hop Ku Ke Zaune A Karkashin Inuwarta?

Eh to gaskiya ka san shi sha’anin samar da kungiya yadda ya ke a cikin al’ummarmu, to amma dai mu na da manya wadanda kusan su ne su ke tace irin Wakar da mu ke yi da kuma Wakar da ya kamata a sakarwa masu sauraro su ji. Amma dukkan shirye-shirye sun yi nisa izuwa yanzu domin ganin a samar da kungiya guda daya wadda  duka za mu kasance a karkashinta.

Cikin Wakokinka Wacce Waka Ce Ka Fi Jin Dadinta Kuma Ka Ke Alfahari Da Ita A Duk Lokacin Da Ka Tuna Cewa Kai Ne Ka Yi Ta?

Eh akwai wakoki na da na ke ji da su kuma ba dan komai ba sai dan ganin yadda jama’a su ka karbi wakokin. To amma ni na fi son wata Wakata mai suna “Mama” saboda a cikin ta ne na ke jinjinawa mahaifiyata bisa irin dawainiya da ta sha yi da ni tun ina karami da kuma irin gudunmawar da ta ke ba ni a cikin rayuwata har izuwa yanzu. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ga cewa ba zan iya kammala kundina ba tare da na saka wannan Wakar ba. Shi yasa na yi Wakar kuma na kirawo ta da suna “Mama”.

Me Ne Ne Zaka Iya Cewa Ka Samu Yanzu Ta Silar Waka Wanda Kuma Ka Ke Alfahari Da Shi?

Alhamdulillah gaskiya ni Waka ta yi min komai domin ta ba ni abinda ban yi zato ba kuma ta kai ni inda ban yi zato ba. Kadan da ga cikin abubuwan da Waka ta ba ni shi ne daukaka da alfarma, Waka ta hada ni da manyan mutane sosai da ban yi zaton samun damar yin alaka da su ba. Waka ta janyo min soyayya da kauna mai yawa daga gurun mutane. Musamman wannnan kundi nawa na “Son Of Jigawa” tabbas ya janyo min zazzafar soyayya musamman a cikin jihata ta jigawa da kuma makotan jihohi. To ba abinda mu dai za mu ce sai godiya ga Allah domin ko iya yanzu mu ka tsaya to Waka ta yi mana komai.

A Karshe Wanne Sako Gareka Zuwa Ga Masoyanka Masu Sauraron Wakokinka?

To ni dai ina fada a duk lokacin da na yi hira da ‘yan jaridu cewa ni masu sauraron wakokina ‘yan uwana na dauke su ba wai masoyana ba kawai. Saboda haka ina yi wa ‘yan uwana godiya ta musamman da irin soyayyar da su ke nuna mana, kuma ina ba su tabbacin in sha Allah ba zan ba su kunya ba. Sannan ina kira garesu da su wanke kunnuwansu domin ina nan tafe da sababbi kuma zafafan wakoki izuwa garesu.

Mu Na Godiya Al-Ameen Kuma Mu Na Maka Fatan Alheri.

Ni ma na gode sosai, kuma ina mu ku fatan alkhairi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: