Connect with us

WASANNI

Gwarzon FIFA: An Fitar Da Sunayen Zakaru Uku

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana ‘yan wasa uku da za a zabi gwarzon dan kwallon kafa na duniya daga cikinsu.

‘Yan wasan sun hada da Virgil Van Dijk na Liverpool dan kasar Holland, da dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo na Portugal da dan wasan Argentina, Lionel Messi na Barcelona.

Van Dijk ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa Turai na bana, kuma shi ne wanda ya fi taka rawar gani a Premier, kuma wanda kungiyar kwararrun ‘yan wasa ta karrama.

Shi kuwa Ronaldo ya lashe kofin Serie A a kakar farko da ya fara takawa Juventus leda, kuma shi ne dan kwallon da babu kamarsa a gasar da aka kammala.

Haka kuma Ronaldo ya jagoranci tawagar kwallon kafa ta Portugal sun lashe UEFA Nations League a watan Yuni, sannan shi ne dan wasan da ya fi yin fice a gasar.

Shi kuwa Messi ya ci kofin La Liga a Barcelona kuma karo na 10, sannan shi ne dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar nahiyar Turai a kakar bana.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: