Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Daure Matashi Wata Uku Bisa Satar Kaza

Published

on

Wata kotu da ke garin Minna ta daure wani matashi mai suna Yakubu Dahiru, a gidan yari har na tsawan wata uku, bisa laifin satar kaza. Da ta ke yanke wa matashin hukunci, alkali mai shari’a Binta Rijau, ta bayyana cewa, za ta yanke wa wanda a ke tuhuma hukunci mai sassauci tun da ya tuba.

Rijau ta bai wa wanda a ke tuhuma umurnin biyar tara na naira 3,000 ko kuma  daurin wata uku a gidan yari. Ana dai tuhumar Dahiru ne da laifukan da su ka hada da hada kai domin aikata laifi, fasa gidajen mutane da kuma na sata, inda ya amsa laifinsa tare da neman sassauci a kan hukuncin da za a yanke ma sa.

Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara Thomas Peter, ya bayyana wa kotu cewa, mutane guda biyu masu suna Yusuf Mohammed da kuma Christopher Yahaya, su ne su ka kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda a ranar 2 ga watan Mayu.

Peter ya kai korafin cewa, ya na zargin wanda a ke tuhuma tare da wasu mutum biyu da balle kofar gidansa, sannan  su ka saci kaza wanda kudinta ya kai naira 2,000.

Lauya mai gabatar da kara ya bayyana cewa, wannan laifi ne wanda ya saba wa sashe na 79, 347 da 288 na dokar fanal kot, inda ya bukaci kotu ta yanke wa wanda a ke tuhuma hukunci kamar yadda sashe na 157 na dokar manyen laifuka ta tanada.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!