Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Binuwe: Manomi Ya Kashe Abokinsa Da Wuka

Published

on

A ranar Litinin ce, wani manomin mai suna Terseer Angbee, ya gurfana a gaban kotun Makurdi, bisa tuhumar sa da daba wa abokinsa wuka har lahira, inda zai cigaba da  zama a gidan yari har sai an samu shawarwari daga ma’aikatan shari’a ta jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, Mai shari’a J. O Anyia bai amshi duk wata hujja da Angbee ya bayar a gaban kotu ba, sakamakon kotun ba ta da hurumin tsallaka iyakarta na wannan shari’a.

Anyia ya bai wa ‘yan sanda umurnin tura fayal din shari’ar ga ma’aikatar shari’a ta Jihar Benuwe domin gudanar da shawarwari. Ya dage wannan shari’ar har sai ranar 26 ga watan Satumba.

Tun da farko dai, lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara Sajan Godwin Ato, ya bayyana cewa, an samu rahoton lamarin ne ta bakin wani mutum mai suna Mista Torngu Mwaikyoga da ke yankin Tse Agu Mbajor Tombo cikin garin Buruku, wanda ya kai labarin lamarin ga ofishin ‘yan sanda na yankinsu. Ato ya zargin Angbee da daba wa mahaifin wanda ya kawo kara, Mwaikyoga Yandeb, lokacin wata sa’insa bayan da wanda a ke zargin ya sare masa bishiyar lemo a cikin gonarsa. Ya kara da cewa, mamacin ya mutu ne a babbar asibitin garin Buruku, sakamakon raunin da ya samu na wannan sukar wuka. Lauyan ya cigaba da cewa, wanda a ke tuhuma ya amsa laifinsa ne bayan da a ka gudanar da cikakken bincike a kan lamarin. Ya ce, wannan laifi ya saba wa sashe na 222 na dokar fanal kot ta Jihar Binuwe ta shekarar 2004 wanda a ka yi wa garan bawul.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!