Connect with us

GAJERAN LABARI

Ministan Cikin Gida Da Shugaban NIS Sun Je Ziyarar Aiki A Katsina

Published

on

A kokarinsa na tabbatar da daidaita al’amuran cikin gida kamar yadda ya kamata, Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola bisa rakiyar Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede sun yi tattaki na musamman zuwa Katsinar Dikko domin yin wata kwarya-kwaryar ziyarar aiki.


Har ila yau, a cikin tawagar Ministan akwai Shugaban Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) inda suka samu kyakkyawar tarba daga tawagar Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari.


A yayin ziyarar dai, tawagar ta kuma ziyarci mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir.
Jami’in yada labarai na Hukumar NIS, DCI Sunday James ya aiko mana da hotunan ziyarar.
Ana ganin dai ziyarar aikin ta kunshi kokarin da Ma’aikatar Cikin Gida ke yi ne na tabbatar da tsaro, bunkasa tattalin arziki da kuma yin aiki cikin gaskiya da rikon amana, kamar yadda aka tsara cimmawa a ma’aikatar jim kadan da rantsar da Aregbesola a matsayin Ministan cikin gida.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: