Connect with us

LABARAI

An Rufe Ofishin Jakadancin Afrika Ta Kudu A Nijeriya-Minista

Published

on

Kasar Afrika ta Kudu ta rufe ofishin Jakadancinta a Nijeriya na wani dan lokaci bisa fargabar kai musu hari sakamakon kashe ‘yan Nijeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu din, kamar yadda Ministar harkokin wajen kasar, Naledi Pandor ya shaidawa kafar watsa labarai ta Reuters.

Ta bayyana cewa; kasar Afrika ta Kudu tana ci gaba da tattauna da hukumomin Nijeriya domin ganin an dawo da zaman lafiya. Inda ta tabbatar da cewa; a dokokinsu bai ba da damar biyan diyyar barnar da aka yi ba sakamakon hare-haren da aka kai wa ‘yan Nijeriya.

Ministar a taron tattalin arziki da ke gudana a birnin Cape Town na kasar, ta tabbatar da cewa za su ci gaba da tattaunawa domin ganin an dakile rikicin tsanar baki da ake yi a kasar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: