Connect with us

RAHOTANNI

‘Yan Sanda Jihar Neja Sun Cafke Magidancin Daya Kashe Abokin Sana’arsa Da Wuka

Published

on

Tundunar ‘yan sanda a Jihar Neja ta kama wani Soja mai mukamin Lance Cpl. Attahiru Jibril, wanda ake zargin ya soki wani mai suna Ali Mohammed da wuka har lahira a kasuwar garin Lambata, ta karamar hukumar Gurara, a Jihar Neja.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar ta Neja, Alh. Adamu Usman, ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a Minna, ranar Asabar.

Wanda ake tuhuman, ya kaiwa wanda ya sokan hari ne in da ya soke shi da wuka har lahira, a sakamakon wata rashin jituwa da ta shiga tsakanin su a cikin kasuwar,” in ji Usman.

Ya ce lamarin ya auku ne a ranar Juma’a.  “Mun yi nasarar kwatan wanda yay i sukar a hannun jama’an da suka kai masa hari a cikin kasuwar, inda muka hanzarta sanar da hukumomin Soji abin da ya auku.

Kwamishinan y ace, wanda yay i sukar yay i ikirarin yana kan aiki na musamman ne a garin Maiduguri, Jihar Borno. Ya kara da cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu da zaran an kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: