Connect with us

WASANNI

Eto’o Zai Iya Taimaka Wa Kamaru Tunda Ya Yi Ritaya – Garba Lawal

Published

on

Tsohon dan wasan Najeriya, Garba Lawal, ya bayyana cewa kwarewa da gogewar tsohon dan wasa Samuel Eto’o zata taimakawa kasar Kamaru idan har ya amince ya karbi tawagar kasar domin ya koyar da ita”

Fittacen dan wasan kwallon kafar Kamaru da ya lashe kyautar dan wasa mafi fice a Afirka har sau hudu, Samuel Eto’o, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekaru 38 a duniya a ranar Juma’a.

A sakon da ya aike ta kafar sadarwar ta Sada zumunta wato Instagram, Eto’o ya ce lokaci yayi da zai bude wani sabon babi a rayuwar sa, inda ya gode daukacin magoya bayan sa da wadanda suka taimaka masa wajen samun nasara a rayuwar sa ta kwallo.

“Dole akwai lokacin da dan wasa yamakata yayi ritaya saboda shekaru ba wasa bane amma ina ganin zai iya zama domin yayi aiki tare da hukumar kwallon kafar Kamaru domin ganin sun cigaba da samun nasara”

Eto’o ya lashe kofin zakarun Turai sau 2 tare da Barcelona, yayin da ya lashe kofin La Liga sau 3 kafin ya koma kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan dake kasar Italiya inda nanma ya lashe kofuna da dama.

A Milan ma ya lashe kofin zakarun Turai da gasar Siriya A da kuma Coppa Italia a shekara guda, kafin ya koma kungiyar Anzhi Makhachkala dake kasar Rasha inda nanma ya buga wasanni da dama duk da cewa bai dade yana zaman Rasha ba.

Daga bisani Samuel Eto’o ya yiwa kungiyoyi irin su Chelsea da Eberton da Sampadoria da Espanyol da Legannes da Konyaspor da Katar Sports wasanni kafin daga baya kuma ya koma kungiyar kwallon kafa ta Fenerhbace da buga wasa a kasar Turkiyya.

Tsohon dan wasan ya kuma lashe kofin Afirka sau biyu da kasarsa ta haihuwa wato Kamaru sannan kuma ya buga wasa da manyan manyan ‘yan kwallo a duniya da suka hada da Ronaldinho da Messi da sauransu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: