Connect with us

KASUWANCI

Hukumar Inganta Rayuwar Al’umma Za Yi Bita Gabanin Damka Kudade

Published

on

Hukumar inganta rayuwar al’umma ta jihar Katsina za ta shirya wani taron horaswa kafin rarraba kudade ga kwamitocin kula da ayyukan inganta rayuwar al’umma domin gaggauta aiwatar da kananan ayyukan.

Mukaddashin janar manaja na hukumar Alhaji Mohammad Dikko Abdul’aziz ya bayyana haka a lokacin rarraba sama da naira miliyan biyar ga al’ummomin kauyukan Duru, Yarkwana, Kofar Fada, Yandaki dake Yankuna kananan hukumomin Mani, Rimi da kuma Kaita.

Mukaddashin janar manajan wanda ya samu wakilcin manajan kudi da mulki na hukumar Alhaji Magaji Yusuf Bakori ya bayyana cewa kananan ayyukan da za’a aiwatar ga al’ummomin da zasu amfana sun hada da gina famfunan hannu gina magudanan ruwa da kuma cibiyoyin kula da lafiya.

Ya tabbatar da cewa hukumar Alhaji Muhammad Dikko Abdul’aziz ya bayyana godiyarsa ga gwamna Aminu Bello Masari bisa bada kason tallafin kudadensa da gaggawa ga bankin duniya domin aiwatar da ayyukan.

Ya gargadi hukumar data bi dukkanin dokokin da aka tsara wajen aiwatar da ayyukan, haka kuma ya shawarce su dasu kare ayyukan daga mabarnata.

Tunda farko a jawabin maraba shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Mani Alh. Shafi’u Abdu Beti wanda ya samu wakilcin Alh. Sada Isa Rawayau ya yi kira ga al’ummar Mani dasu hada hannu da hukumar inganta rayuwar al’umma domin amfana da shirye-shiryenta.

Alh. Sada Isah Rawayau ya ce shaida kyawawan ayyukan hukumar da al’ummar yankunan karkara ke bukata.

Daga cikin abubuwan da aka gudanar a wajen taron sun hada mika chakin kudi ga al’ummomin kauyukan guda (3) wanda mataimakin shugaban riko na karamar hukumar mani Malam Shehu Kabir ya aiwatar.

Haka kuma, kungiyar cigaban al’ummar garin Tsagero na shirin yin hadin guiwa da hukumar inganta rayuwar al’umma domin bullo da ayyukan inganta rayuwar al’ummomi domin cigaban gundumar.

Shugaban kungiyar Alh. Saleh Aliyu Tsagero ya bayyana haka a wajen wani horo da yayin da kungiyar da ya gudana a fadar maji dadin Katsina hakimin Tsagero.

Alh. Saleh Aliyu Tsagero wanda kuma shi ne shugaban ma’aikata na karamar hukumar Charanchi ya ce kungiyar zata karbi gudummuwa daga al’ummar yankin domin bada kudaden kasonsu don aiwatar da ayyukan.

Ayyukan kamar yadda ya ce sun kunshi samar da ruwa, gina makabarta, gyara da kuma katange kuma giwaye cibiyar kula da lafiya dake garin Tsagero domin bunkasa sha’anin kiwon lafiya a gundumar.

Haka kuma Alh. Sale Tsagero ya bayyana shirye shirye da kungiyar ke yi na gina magudanan ruwa a bayan cibiyar kuma da lafiya dake yankin domin kare ambaliyar ruwa.

Kazalika ya bayyana godiyarsa ga majidadin Katsina hakimin Tsagero Alh. Garba Usman Nagogo da shugaban kwamitin riko Alh. Abdullahi Aliyu Turaji bisa gudummuwar da suke bayarwa wajen cigaban yankin.

A tsokacinta, jami’ar kula da cibiyar kiwon lafiya ta yankin Hajiya Hafsat Sule  ta yabama ‘ya’yan kungiyar bisa gudummuwar da suke bayarwa wajen tafiyar harkokin asibitin.

Majidadin Katsina wanda ya samu wakilcin Lamido Lemamu Tsagero ya tabbatar da goyon bayan masu rike da sarautun gargajiya ga shirye shirye da manufofin kungiyar na kawo cigaba mai ma’ana a yankin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: