Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Legas: Tirela Ta Murkushe Uwa Da Diyarta A Birnin Ikko

Published

on

‘Yan sanda sun damke wani direban tirela mai suna Soje Ojo, bisa murkushe wata mata mai suna Ajoke Ogunremi tare da yarinyarta Aina, har lahira a kan kan titin da ke yankin Ojuelegba cikin Jihar Legas. Haka kuma an damke wani dan acaba mai suna Paul Onyeka, domin ya na da laifu wajen gudanar da hatsarin.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, matar da diyarta sun zo tsallake hanya da ke kusa da barikin sojoji na Albati Barracks, a ranar Asabar, ba zato ba tsammani sai dan acaba ya biyo ta tsakanin su ya na kokarin tsallake hanyar. Lokacin da su ka yi kokarin guje wa dan acaban, sai su ka fada wa tirelan mai zuwa, inda ta murkushe su har lahira. Nan take Aina ta mutu, yayin da mahaifiyata a ka tabbatar da mutuwarta a asibiti lokacin da a ka garzaya da ita.

Wani mai motar haya wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Deji Olusesan, ya bayyana wa manema labarai cewa, Ojo da Onyeka sun gudu, amma daga baya ‘yan sanda daga yankin Surulere sun damke su.

Ya ce, “Hatsarin ya afku ne a ranar Asabar da safe. Matar ta na son ta shiga cikin barikin Albati Barracks, inda ta yi kokarin tsallake titi tare da yarinyarta. Lokacin da ta tsallaka gefe daya na hanyar, ba zato ba tsammani sai ga dan acaba a guce. Sun yi kokarin komawa baya, sai tirela da ke zuwa ta murkushe su. Nan take yarinyar ta mutu, yayin da a ka dauki uwar zuwa asibiti, inda daga baya na samu labarin mutuwarta,” in ji shi. 

Wani daga cikin jami’an bayar da agajin gaggawa wadanda su ka isa wurin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa, hatsarin ya rutsa da tirela mai lamba kamar haka MUS 834 DG da kuma babur kirar Mad mai lamba kamar haka Lagos AKG 347 GF. “Mutum biyu wanda su ka hada da wata mata da kuma diyarta sun mutu a wannan hatsari, inda a ka ijiye gawarsu a asibiti. Daga baya an bayyana sunan matan da Ajoke Ogunremi ‘yar shekara 43, yarinyar kuma ta na da suna Aina mai shekaru 10,” in ji jami’in bayar da agajin gaggawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya bayyana cewa, an damke wadanda a ke zargi da sabbaba wannan hatsarin. Ya kara da cewe, “hatsarin ya rutsa da wata motar tilela wanda wani mutum mai suna Soje Ojo ke tukawa da wani dan acaba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar uwa da kuma diyarta mai shekaru 10. Tirelan da dan acaban su na tafiya ne a hanya daya, inda uwar da diyanta su ka yi kokarin tsallake hanyar. “Sun dawo baya kenan sakamakon dan acaban mai suna Paul Onyeka ya yi kusa da su ya na kokarin buge su. Sai su ka fadawa tirelan, inda ta murkushe uwar da kuma yarinyar har lahira.

“Nan take yarinyar ta mutu, yayin da mahaifiyarta ta mutu lokacin da ta ke amsar magani a asibiti. An dai ijiye gawarwakinsu a dakin ijiye gawarwa ki da ke asibiti.”

A wani lamari irin wannan kuma, wani mutum mai suna Bashiru Ahmed dan shekara 25 da haihuwa, ya na cikin tafiya a kasa kenan, sai wani dan acaba mai suna Friday Augusta dan shekara 30, ya murkushe shi har lahira a tashar mota ta Cappa da ke kan babbar titin Oshodi zuwa Apapa. Ahmed ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Legas da ke Idi-Araba, sakamakon mummunar rauni da ya samu. 

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewa, an ijiye gawar mutumin a dakin ijiye gawarwaki da ke asibiti.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!