Connect with us

LABARAI

Shugaban Karamar Hukuma Ya Ja Hankalin Malamai Kan Zaman Lafiya

Published

on

Shugaban kwamitin karamar hukumar Rimi ya jaddada bukatar malaman addini su fadakar da mabiyansu muhimmancin zaman lafiya da kuma kasancewar kasar nan baki daya.

Alh. Abdullahi Turaji ya yi rokon a lokacin taron kwamitin malaman na munazzamatul fityanul Islam da aka gudanar a karamar hukumar Rimi.

Mai Abdullahi Turaji ya tabbatar da cewar zai bawa kungiyar goyon bayan dace ya ce malaman addinai na da rawar da su ke takawa na wanzuwar zaman lafiya a cikin al’umma.

Dan majalisar dokokin yankin Alhaji Suleiman Abubakar Karau ya bayyana godiya ga kungiyar dangane da shirya taron a yankin.

Kasidun da su ka gabata a lokutta daban-daban Malam Musa Alkali da Malam Hamza Safana sun bukaci al’ummar musulmi su dage wajen gudanar da sallolli biyar na yau da kullum, a lokutan bukukuwan radin suna da daurin aure da kuma sallar juma’a domin dorewar zaman lafiya a kasa bakidaya.

Gwamnatin jahar Katsina ta kashe naira miliyan dubu dari uku da saba’in 370 wajen sanya litattafan karatu da sauran kayan koyarwa a wannan shekarar.

Kwamishinan ilimi farfesa Badamasi Lawal Charanchi ya fadi haka a lokacin raba litattafan dubu tamanin da shidda da dari biyar ga daraktocin shiyyoyi ilmi sha biyu domin su rarraba ga makarantu.

Kwamishinan ilimin ya na nanata cewar rabon litattafan karatun na daga cikin kokarin gwamnatin jahar Katsina na samar da ilimi mai ingancinta hanyar samar da yanayin koyo da koyarwa mai kyau a makarantu.

Litattafan karatu da aka raba sun hada da litattafan tarihi, da na koyan na’ura mai kwalkwalwa, da na koyanta a ciki da physics, chemistry, biology, English, literature da koyon harshen turancin da lissafi da cibic education da sauaransu.

Ya bukaci shuwagabannin makarantar da su gaugauta rarraba litattafan karatun ga daliban.

Sun kuma jaddada muhimmancin gudanar da samar da tsaro da bukatar jama’a su jadda biyayya ga shugabanci da kuma iyaye.

Sun godewa shugaban kwamitin rikon karamar hukumar dangane da daukar nauyin gudanar da taron wanda a ka kammala cikin lumana.

Sauran wadanda su ka yi jawabin sun hada da Dayyabu Imam, Malam Umar Janbango da manyan Imaman da kuma malamai.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: