Connect with us

Uncategorized

Gidauniyar Gwagware Ta Raba Kayan Abinci Ga ‘Yan Gudun Hijira A Katsina

Published

on

Gidauniyar Gwagware ta rarraba kayan abinci ga ‘yan gudun Hijira wadanda bala’in ‘yan bindiga ya rutsa da su a kananan hukumomi tara da ke fama da tashe-tashen hankula a jihar Katsina.

Kananan hukumomi da wannan iftila’I ya afkawa sun hada da karamar hukumar Sabuwa da Dandume da Faskari da Kankara da Danmusa da Safana da Kurfi Da Batsari da kuma Jibiya wanda dukkan ana kai wannan hare-hare na wuce gona da irin akan jama’ar da ba su ji ba su gani ba.

Da yake magana a wajan bika wadannan kayyaki, a garin Batsari, jigo kuma ginshikin wannan gidauniya Dakta Dikko Umar Radda (Gwagwaren Katsina) kuma shugaban hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu SMEDAN ya ce sun zo Batsari domin su jajantawa jama’a akan wannan masifa ta samesu.

Ya kara da cewa sun je sauran kananan hukumomin guda takwas, ya ce lura da hakkin da Allah ya dora masa na shugabanci, saboda a cewarsa hidimar tsaro hakki ne da ya shafi kowa da kowa wajan bada gudunmawa a samu zaman lafiya.

Alhaji Dakta Umar Radda ya bayyana cewa sai ka kwatanta cewa wannan lamari kai ya shafa kafin ka ji karfin halin tausayawa wadannan mutane da aka jarabta da wannan matsala ta rashin tsaro..

“Muna ji muna gani, masu arziki a wasu garuruwa sun talauce sun kuma suna bara, saboda halin da suka shiga, a dalilin haka muna da hakki da zamu taimaka da abinda muke da shi ga wadannan mutane domin a saukaka masu radadin wannan iftila’I” inji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga sauran masu rike da mukamai a matakin tarayya da jihohi da su taimaka da dan abinda suke da shi ga wadannan bayin Allah, ya kara da cewa ba sai da yawa ba ko ya ya idan kana da shi ka taimaka.

“Tabbas wannan lamari jarabta ce daga Allah, abinda kawai ya rage mana shi ne Malamai su cigaba da koyar da jama’a yadda za su tuba wajan Allah tuba ta hakika, da niyar Allah ya kawo saukin wannan al’amari a wadannan kananan hukumomi da jihar Katsina da ma arewa baki daya..” Dakta Dikko ya bayyana

Tunda farko da yake nasa jawabin mai kuda da gudanawar wannan gidauniya Alhaji Kabir Amoga ya ce sun zo Batsari ne ba domin siyasa ba, sun zo ne su taimakawa wadanda suke da bukatar taimako, kamar yadda suka je sauran kananan hukumomi takwas.

Ya ce wannan taimako na da nufin tausayawa wadannan ‘yan gudun Hijira da bala’in ‘yan bindiga ya raba da muhalinsu ba don suna son haka ba, shi yasa ma shi gwagware Dakta Dikko Umar da kansa ya zo Batsari domin yin wannan jaja.

Alhaji Kabir Amoga ya ce kowace karamar hukuma tara da suka je sun bada buhunan abinci 100 da suka hada da Gero da Dawa Da Masara da kuma wake tare da gidajen sauro domin amfanin jama’ar da ke wannan wuri.

Kazalika ya kara da cewa ya zuwa yanzu shiri ya yi nisa a karkashin jagoranci madugu uban tafiyar gidauniyar gwagware wajan shirya addu’o’I na musamman a dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina domin ganin an samu saukin wannan bala’I da ya fadawa jihar Katsina.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!