Connect with us

KIWON LAFIYA

Kasar Uganda Za Ta Fara Gwajin Allurar Rigakafi Ta Ebola

Published

on

Kasar Uganda ta bayyana fara amfani da gwajin allurar rigakafin cutar Ebola, wanda za a yi amfani da shi a Jamhuriyar Dimikaradiyar Congo mai makwabtaka da ita, inda annobar ta Ebola ta hallaka mutane dubu 1 da 800 cikin shekara daya kacal.

Shi dai aikin gwajin maganin rigakafin hana kamuwa da annobar ta Ebola mai suna ‘MBA-BN’ da kamfanin hada magunguna na Amirka Johnson & Johnson ya yi zai kai tsawon shekaru 2 ana yin aiki da shi ko kuma yana yin aiki a jiki, kamar dai yadda sanarwar da hukumar binciken magunguna ta kasar Uganda (MRC) ta sanar.

Hukumar ta MRC ta bayyana cewar tafiyar da aikin bada maganin rigakafin, zai kunshi kimanin jami’an kiyon lafiya dubu 8000, wadanda kuma sune suke cikin sahun gaba, a cikin aikin sun hada ne da malaman tsafta, da na motocin daukar marasa lafiya, da kuma masu kula da dakunan ajiye gawarwaki, sai kuma masu rufe wadanda suka mutu a lardin Mbarara dake yammacin kasar ta Uganda.

Zuwa yanzu dai babu maganin da zai hana kamuwa ko kuma warkar da cutar Ebola a duniya, sai dai ana da kyakkyawan fatar samun maganin, la’akarin da cewa akwai wasu jerin magungunan hana kamuwa da cutar ta Ebola na gwaji da ake kan amfani dasu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!