Connect with us

RIGAR 'YANCI

Za Mu Shawo Kan Matsalolin Tsaro A Bauchi – Gwamna Bala

Published

on

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad yayi alkawarin bayar da gagarumar gudunmawarsa wajen shawo kan matsalolin tsaro da aikace-aikacen ta’addanci da ke addabar wasu sassan jihar.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan yada labarai, Muktar Mohammed Gidado, ya ce; Gwamna Bala, ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya amshi bakwancin sabon Kwamadan Aiyuka na musamman na Rundunar Sojin sama da aka turo jihar aiki jihar Bauchi a lokacin da shi da ‘yan gawatarsa suka ziyarci gwamnan a gidan gwamnatin jihar.

Sanata Bala Muhammad ya shaida cewar tunin suka nemi shugabannin sassan tsaro da su yi nazarin hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro da yadda za a kawo karshensu, kamar garkuwa da mutane, fashi da makami da sauransu.

A cewarshi, jihar tana dan fuskantar wasu ‘yan kananun matsalolin tsaro wanda akwai gayar bukatar hada hanu wuri guda domin shawo kan matsalolin domin dawo da jihar zuwa matakin da take kan na ci gaba da ribantar dumbin zaman lafiya.

Bala ya baiwa sabon kwamandan da ke kula da aiyuka na musamman da aka turo jihar da cewar gwamnatinsa za ta bashi dukkanin hadin kai da goyon baya domin ya samu nasarar cimma aiyuka da ke kansa na tabbatar da tsaro, ya ce sauran bangarorin tsaro ma za su samu goyon bayansa ta fuskacin samar musu da muhallan da suka dace da aiyukansu.

Gwamnan yayi amfani da wannan damar wajen jinjina wa kokarin shugaban sojojin saman Nijeriya, Air Marshal Sadik Baba Abubakar a bisa kokarinsa na samar da barikin sojin sama a Bauchi, a cewarshi, hakan ya kawo ci gaban tsaro ba kawai a jihar ba, arewa maso gabas gaba daya tana cin gajiyar wannan barikin.

Ya kuma ce, samar da barikin ya kara bayar da dama wajen bunkasa walwalar rayuka da dukiyar jama’a, gami da kuma tabbatar da kyauta da kiwon lafiya, ilimi da kuma kare dukiyoyin jama’an jihar.

Tun da farko, sabon shugaban sashin musamman na rundunar sojin saman Nijeriya a Bauchi, Air Bice Marshal, James Gwani ya nemi samun hadin kai da goyon baya domin ya samu nasarar cimma muradinsa na bayar da cikakken gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da tsaro.

A cewar shi; tabbatar da tsaro da zaman lafiya zai taimaka wa gwamnan sosai wajen bashi damar da zai kai ga samun nasarorin tsaretsarensa da shirye-shiryensa na tabbatar da gina jihar da kuma bunkasa ta.

Air Vice Marshal James Gwani ya kuma nemi yin aiki tare da gwamnan jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin taimaka wa bangarorin tsaro don su samu zarafin aiwatar da aiyukan da ke kawukansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!